Musabbabi Book 1

Page 112

by @yargidanimam

wasu ma cewa za su yi ya sayar da kaddarorinsa ne,ya yi iskancinsa, babu wanda zaiyi zargin kece kika kwashe dukiyarsa,” Hajiya Kilishi ta yi dariya sosai ta ce “Amma haj ban taba tunanin ki na da kaifin basira haka ba, idan ka kashe makiyin ka ma, ai ka taimaka masa ne, gara ka'aje shi ka yi ta kallon sa yana wahala a rayuwarsa, don haka shawararki ta yi, na kuma dauketa, ki na kuma da tukuici na musamman' Hajiya Rakiya ta ce "To godiya na ke babbar giwa, musaddik din me da zai dinga tayar miki da hankali”

Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce "Amma ina fatan za ki ci-gaba da rike min sirrina kamar yadda ki ka saba, kada wanda ya ji ko ya gani, mu haka mu binne, kamar yadda muka saba”

Haj Rakiya ta yi dan murmushi ta ce "Haba, haba, ai ba ki da wata matsala in dai nice, ki sha kuruminki, babu me ji ai tsakanin mu ya wuce haka” Haj kilishi ta sauke ajiyar zuciya ta na jin tamkar ta gama mallakar komai na daga cikar burinta a duniya.

daga nan suka ci-gaba da tattaunawa akan yadda komai zaibtafi yadda suke so ba tare da wata matsala ba.