Page 113
Washegari kuwa da taimakon rakiyar haj Rakiya suka tafi rugar Mai Rakwacam dauke da bukatunsu, da fatan samun dacewa. Mai Rakwacam ya dauk tsawon lokaci yana bincikensa, kafin ya dubi Hajiya Kilishi ya ce, '"Aiki zai yiwu, bukata kuma za ta biya, ki aje Naira dubu dari biyu da hamsin, za' a sayi kayan aiki." Nan da nan Hajiya Kilishi ta Balle jakarta ta aje masa kudin, ya kara kallonta ya ce "To ku tashi ku tafi, jibi goshin magariba ki dawo”
Haj Kilishi ta yi godiya, suka tafi Kwanaki biyu tsakani goshin magariba kamar yadda me Rakwacam ya bukata. Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka isa rugar, sun tadda Mai Rakwacam ya kammala duk mugun aikin da zaiyi akan bukatar su.don haka Ya dauko wata bakar laya da ta ji surkulle, ya dubeta yace ta sami kasan jijiyar bishiyar kuka ta binne hade da wani dan karamin kasko daya ji daure-dauren bakin zare, duk jikinta an zaneta da Sunan Musaddik, ya ce ta hada da layar ta binne, da zarar ta binne aiki ya kammala. Babu wanda zai raba Musaddik da Shaye-shaye da lalacewa, sai ranar da aka tono wannan layar da kaskon. Don haka ta san yadda za ta binne da kuma inda za ta binne.domin ana son dadaddiyar kuka da ta dade. Ya kara da cewa, ba zai karbi ko sisi ba, sai aiki ya ci. Daga nan za ta dawo ta cake masa Naira dubu dari uku cif! Hajiya Kilishi ta karbi komai ta