Musabbabi Book 1

Page 114

by @yargidanimam

yi godiya tare da alkawarin dawowa ta ba shi hakkinsa da zarar bukata ta biya, daga nan suka dauki hanyar gida

Suna cikin tafiya ne. Hajiya Kilishi ta dubi Hajiya Rakiya ta dan rage gudu fuska cike da farinciki ta ce "Yanzu ina za mu samu bishiyar kuka, inda za'mu binne wannan asirin?" Hajiya Rakiya ta yi murmushi ta ce. "Dadina da ke mantuwa, ai ni tunda ya ambaci bishiyar kuka, na ji na sami kwanciyar hankali , kin manta rikakkiyar bishiyar kukan da ke bayan gida na, abubuwa nawa muka binne a kasanta, tun marigayi megidanki na raye,”

Hajiya Kilishi ta fashe da dariya ta ce "Godiya “ Anyi haka, godiya na ke da samun aminiya, mai share hawayen kuka na, yanzu kawai mu wuce gidan naki mu aiwatar da aikin kafin na wuce gida” Haj Rakiya ta yi dariya tace “Angama kawata”.

Sun isa dare ya yi, gari kuma ya yi duhu, Hajiya Rakiya ita' ce me haska ma Haj kilishi bakin bishiyar da hasken wayarta. Hajiya Kilishi kuma na aikin haka, sai da ta haka rami me zurfi. Sannan ta binne kaskon da layar. Babu Wanda ya gan su har suka gama, suka tafi.hankali kwance kamar wadanda su ka aikata abinda ya dace, Allah kasa mu fi karfin zuciyar mu, yasa duk runtsi mu tsira da imanin mu.

Kwanaki biyu tsakani, sai ga Hannatu hajaran majaran tana gaya ma Hajiya Kilishi ba za ta koma. gidan Musaddi& ba, domin jiya kwana ya yi yana shaye-shaye, ta ce dama ya iya shayc-shaye ne? Mutumin da ko taba ba ta taba ganin ya sha ba,