Page 115
amma rana amma abin tsoro da mamaki sai gashi rana tsaka ta gan shi cikin wannan mummunan halin. Hajiya Kilishi ta fashe da dariya, ta mike tayi rawa, ta yi juyi, ta daga hannu tana yi ma Allah godiya tare da yi ma kanta kirari na sharri. Hannatu ta yi galala tana kallonta cike da mamaki Hannatu tace
“ Ya na ga ki na murna Inna, wannan fa magana ce ta canja sabon babi magana ce ta lalacewar rayuwar Musaddik da ni kaina” Hajiya Kilishi ta koma ta zauna, tana Fadin “ waye yace miki haka Lalacewar rayuwarsa dai, ina ruwan ki, ko kin manta tun farko na gaya miki wannan aure ne na dan lokaci; aure ne kuma na samun arziki, ko kin yi kuskuren fara sonsa ne?" Hannatu ta girgiza kai ta ce "Ban fara sonsa ba gaskiya amna a zahiri na fara tausayinsa, saboda in dai rayuwar da ya fara a yanzu akanta zai cigaba da tafiya to babu abu daya na alheri da zai zo gabansa a duniya “ .Haj kilishi ta saki tsaki tace “ ke dube ni nan bana son shirme To shi ma tausayin ki yi gaggawar cire shi a ranki, domin daga tausayin ne ake samun soyayya, auranki da shi kuma ya kusa zuwa karshe saura kiris Don rayuwarki dama ba ta dace da ta Sa ba,dukiyarsa da son cikar burina su ne musabbabin auranku, kamar yadda cikar burina, zai Zama musabbabin rabuwarku”. Hannatu ta numfasa, ta dade tana ganin mata marasa imani, ciki har da mahaifiyarta, amma ba ta taba ganin mara imani irin Hajiya Kilishi ba, a duk lokacin da ta yanko wani sharrin ta kan yi zaton ko shaiden ne ya fito a suffarta.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️