Musabbabi Book 1

Page 126

by @yargidanimam

Mama Hauwa ta mika hannu saman firij ta dauko wata bakar leda, ta fice ita da Na'ima. Afrah ta mike da nufin rakasu, amma ga mamakinta suna fitowa, sai ta ga Mama Hauwa ta durkusa ta kwashe tarkacen kayan mayen da ta tara, ta zuba su a cikin ledar. A nan ne Afrah ta dubeta ta ce "Mama me za ki yi da su?” ta karasa magana tana kokarin gyara tsaiwarta.

Ta balla mata harara ta ce “zan kaima mahai finki tsarabar da na samo daga gidanki ne, ina ganin zai fi gamsuwa da halin da kike ciki idan ya gani”. Gaban Afrah ya yi mummunan faduwa, da sauri ta karasa gabanta ta ce cikin magiya da nuna tsananin damuwarta "Don Allah, Mama kada ki yi min haka, kada ki tayar ma da Baba hankali, meye amfanin yin hakan?" Ta kara sakar mata harara ta ce “Tashin hankalin me zai yi, bayan duk wanda ya sai rariya, ya san za ta zubar da ruwa, ke mu tafi da Allah" ta fada cikin rashin nuna damuwa. tasa hannu ta jawo hannun Na'ima suka fice ba tare da ta damu da magiyar da Afrah take yi mata ba. Haka Afrah ta kasance a cikin bakinciki, Bayan tafiyarsu Mama Hauwa da kyar ta gama wankin, amma ta kasa yin guga, haka ta ninke ta ajiye, hatta abincin da ta yi, ta kasa ci, saboda damuwa, ga Musaddik tun safe daya fita, har yanzu bai dawo ba.

Ta bangaren Mama Hauwa kuwa, haka ta kasance cikin wani irin nishadi da farinciki,tun bayan komawarta gida. ta kosa kwarai Mallam Mahmud ya dawo ta zazzage tanadin rashin mutuncin da ta tanadar masa. Har sai da Malam Mahmud ya dawo, bayan sallar Issha'i, ya zauna kan tabarma, a kofar dakinsa inda ya saba zama .