Musabbabi Book 1

Page 127

by @yargidanimam

Mama Hauwa ta kawo masa tuwo, zai fara ci kenan, saboda wulakanci da rashin mutunci, kawai sai ta koma ta zauna kan kujera 'yar tsugunno tana murmushi tace “Ba ka tambayeni ya na baro Afrah ba, bayan ka san na ce maka zan je gidanta yau?" Ya dan muskuta ya na dan murmushi yace "'Na san lafiya lau take ai, shi ya sa ban tambayeki ba, kuma ko kadan, kada ki bari jama'a su san cewa sai yau ki ka je gidan Afrah, domin abin kunya ki ka yi. Ace tsawon wannan lokacin ba ki je kin ga dakinta ba, sai yau." Ta tabe baki ta ce "Idan jama'ar suka ji, me za su yi min? Dole ne na je akan lokaci? Ba sai na sami lokaci ba, sannan zan je." Ya juya kan tuwonsa zai fara ci, ba tare daya Kara magana ba. Amma sai ta Kara katse shi, tamkar tana yi masa bakin-ciki da cin tuwon tace “Na je na tadda ita tana ta akin yima mijinta wanki, gama tsarabar dana taho maka da ita daga cikin wadanda yake ragewa a aljihun wandonsa”, Malam -Mahmud ya juya yana kallon kayan mayen da take zazzage masa a gaba, a fusace ya zaro idanunsa alokacin da ya gama fahimtar ko me take juye masa a kasa, rai a bace yace

"Meye haka Hauwa?"cikin nuna halin ko’in kula mama Hauwa tace

" meye kuwa da ya wuce Kayan mayen Musaddik, na taho maka da su domin ka gani". Ya yi mata wani mummunan kallo ya ce. "Amma Hauwa ba ki da mutunci, to yanzu da ki ka kwaso min, idan na gani, me zan yi, meye kuma amfanin kawo min?"