Page 128
Ta tabe baki ta na sa hannu tana kara tona kayan,tace “Haka ne fa kuma, babu amfanin na kawo maka, tunda ka riga ka sani, ka san komai, amma ka dauki 'yarka ka ba shi,Hakika ni ma na fara tunanin akwai abinda ka ke hange a gun Musaddik, da ya sa ka ba shi auran 'yarka, don idan ba hangen wani abu ba, na dukiya ban ga dalilin da za ka kashe ma 'yarka rayuwa da auran Musaddik ba, don banga amfanin da hakan zaiyi maka ba daga kai har Halimar me mara maka baya” Malam Mahmud ya buga tsaki ya ce "Dukiya, dukiyar banza, me Musaddik din ya aje? Kin sani, na sani. Musaddik komai nasa ya Kare, tabbas ina da manufar hada su aure. Amma ba irin manufar da ku, ku ke tunani ba, don haka Afrah 'ya ta ce, ni na ga damar yin hakan da ita. Kuma ina gargadinki da ki fita harkata da ta 'yata, tunda ba 'yarki bace balle ki ce ban isa na yi iko da ita ba, ita taki yar ai na bar miki kayanki ko, to babu ruwanki tsakanina da yata, kuma ko dar banji ba don naga wannan abin, illa kaimi da ki ka kara min na kara jajircewa da yi ma yayana addu’a”. Mama Hauwa ta mike "Eh ai dama bance yata bace, ba kuma na fata ta zama yar tawa, ni ma karambanina ya jawo min, ina ruwana kuwa,idan musaddik ya na iyawa ma ya zama dan kashin kasuwa karewar iskanci” Ya kara watsa mata wata uwar harara yace "Na ji, ki tafi ki ba ni waje, kuma kada ki kara takawa gidan Afrah balle har ki je ki sa idon daukar magana, babu ruwanki da ita, balle mijinta yadda ba mu kasa da ke ba don Allah kada ki dauka”,Ta yi shewa ta ce "To sai me? Sai ka ce wani mijin kirki, gidan Afrah kuma ba zan kara zuwa ba, tunda ba aljanna ake rabawa a can ba, ga kayen mayen nan, idan ka gama gani, sai ka san inda za ka aje". Ta saki tsaki ta shige daki ta rufe kofarta