Page 129
Malam Mahmud ya kurawa kayan mayen ido,idanunsa cike da hawaye, zuciyarsa tana tafasa matukar tafasa damuwa ta kara mamaye shi. Hakika ba haka ya so rayuwar 'yarsa ta kasance ba, amma babu yadda ya iya, haka Allah ya kaddara musu duka. Tausayin Afrah ya kara kama shi, a hankali ya janyo kayan, ya kwashe ya maida su cikin ledar, cikin matsanancin tashin hankali, ya ture kwanon tuwon gefe, ya tashi ya nufi bandaki, ya jefasu cikin masai. Sannan ya shige dakinsa ya kulle kofarsa ba tare daya ci tuwon ba. Duk da yunwar da yake ji, ya kasa runtsawa domin yadda ya ga rana haka ya ga dare, sai dai ya yi kokarin raya daren ta hanyar yin nafilfilu wanda duk addu’ar kan Afrah da Musaddik ta kare
Washegari kuwa shi ma din cike da damuwa Mallam Mahmud ya je gidan Inna Halima, ya gaya mata komai gami da yi mata umarnin ta je ta kara karfafama Afrah guiwa tare da ba ta hakuri. Inna Halima ba ta yi kasa a guiwa ba, ta nemi izinin mijinta, ta tafi gidan Afrah. Wanda Afrah ta ji dadin ganinta, amma tana fara yi mata maganar Musaddik. Ta san Mama Hauwa ta je ta yi abinda take zaton za ta yi. Ta dubi Inna Halima ta ce "'Inna me zai sa ku tashi hankalinku, don kawai Mama Hauwa ta je ta gaya maku abinda ku ka riga ku ka sani? Kun san Yaya Musaddik ba mutumin kwarai bane, akan wannan dalili ne ma na aure shi, to me zai sa ku damu? Bayan addu'a kawai ya kamata ku bi mu da shi ba damuwa ba” Inna Halima ta jinjina kai , sha’awar Afrah da halayenta suka kara kamata tace “Maganar ki haka take Afrah, don haka Allah ya yi maku albarka, ya taimake ki akan duk abinda ki kasa a gaba, mun gode da hadin kanki, Allah yasa wata rana farinciki ya wanzu acikin rayuwarki”.