Page 130
Afrah ta sauke numfashi a hankali Tace "Amin Inna". Inna Halima Ta dan dubeta tana kokarin gano wani abu, tace "Amma Afrah yaya zamanku, ki na jin jindadin zama da shi, kuma ki na ganin akwai alamun yana rage mugayen dabi'unsa, ma'ana ana samun canji ko yaya ne kuwa?” Afrah ta dan yi murmushi me kama da yake sannan tace "Inna ai Yaya Musaddik yana da dadin zama Kwarai, kuma ana samun canji da abubuwa da dama akan halayensa, sai dai mu ci-gaba da addu'a kawai domin babu abinda ya gagari Ubangiji “ Fuskar Inna Halima ta cika da fara'a da jindadin maganar Afrah, ta shiga fadin "'Alhamdulillahi. Allah ya kara taimakon mu akan wannan kyakkyawar niyyar ta mu. Allah ya saka miki da alheri Afrah”,Duk wasu tambayoyi da Inna Halima ta yima Afrah, tana kokarin ba ta amsar da za su sata farinciki ta kuma yi sa’a har ta bar gidan, ba ta fahimci karya ko daya a cikin maganganun Afrah ba.
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM