Musabbabi Book 1

Page 131

by @yargidanimam

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, yau fari gobe baki, tuni Afrah ta aje maganar wai dole saita sami kulawa ko nunin soyayya daga Musaddik domin tasan babu wannan a gabansa, A hankali har garar da Malam Mahmud ya yima Afrah ta Kare, har ta kai abincin da Afrah zata ci ya fara yi mata wahala, tunda Musaddik baida ko halin da zai iya ciyar da ita, idan ma ya samu abinda zai ciyar da itan abin takaici duk sai dai , su Kare a wajen sbaye-shayensa da kuma bawa sauran mutane domin duk abinda ya samu shaye shaye kan ci rabi jamaa kan ci rabi,don akwai fa kyauta da ka tambaye shi in dai yana da shi zai dakko ya baka, ko da zai zauna baida ko sisi. Har kuma yanzu ya kasa jin aransa shi ma magidanci ne. Ta Bangaren Hajjya Kilishi kuma ko farantin daya na abinci ba ta iya ba ta balle harta sa ran zata iya taimaka mata da wanda zata dafa. Ko cikin gidan ta shiga takan yi kokarin maidata baiwa ne ta hanyar sanyata yin aikin gidan duk da ga masu yi mata aiki nan, sannan ga cin zarafi da wukakanci na ba gaira ba dalili, wanda Afrah take ganin ba zata iya dauka ba, domin dai a tsaye take bata jurar duk wani wulakanci daga Haj kilishi shi yasa ta ja kanta ko cikin gidan ta rage shiga, babu kuma yadda za’ayi komai wuyar da take ciki ta bude baki ta roki haj kilishi wani abu domin tasan tozarta ne a gareta da mijinta, ya kuma dole ta boyewa Haj kilishi gaskiyar halin da take ciki saboda bata son ta yi farinciki ko kadan akan yanayin zamansu da musaddik, Amma ko da ta daina shiga bangaren Haj kilishi, hakanan za ta turo masu aikinta su kirata. Idan taje kuma ta sata aiki , Afrah takan dage ta boye jin zafinta ta yi mata aikin, amma a gabanta zaa gama abinci, Haj kilishi tayi mirsisi ta hanata a zuba mata, haka zata dawo bangarenta da yunwa,ta rasa me yasa take mata wannan mugun horon, sai a wata rana ta gane dalilin da yasa take mata haka. Zata shiga bangaren Haj kilishi kenan ta ji tana waya da yarta Hassana, tana gaya mata yadda ta maida Afrah me aikinta da hanata abinci da take yi ko ta yi mata aikin, Afrah na tsammanin Hassana ta tambayeta dalilin da yasa bata bata abinci ne yasa Haj kilishi tace “Ai yarinya ce me shegen zurfin cikin tsiya, duk yadda na so naji kanta da Musaddik ta ki kullum nunawa take komai lafiya, na kuma san ko abinci baya bata shi yasa nake mata haka ina son ta bude baki da kanta ta roke ni na basu abinda zasu ci amma ta ki”.

Jin hakan yasa Afrah ta juya ta koma bangaren ta tare da shan alwashin har abada ita da ta nemi taimakon wani abu daga Haj kilishi. Ta kuma kara dauke kafa a sasan ko ta aiko a kirata takan kirki bata da lafiya. Ta fita harkarta gaba daya,wanda hakan ya kara tunzura Haj kilishi sosai.

Lokuta da dama idan Afrah taje islamiyya ya sayyadi Habib ya kan yi mata kyautar kudi ba don ta roka ba sai don kawai yana ganin cancantar hakan a matsayinsa na yayanta a yanzu. Sai dai ko shi daker take amsa sai ta ga bata da wata mafita sannan take amsa. Wani lokacio ne ma idan ta je Islamiyya. don kudin daya ba ta gudunmawa ma da ta yi niyyar tayi sana’a da su tuni suma suka Kare, saboda zararsu da take yi tana yin hidimar gidan. Da kuma Musaddik ya fahimci akwai dan wani abu a hannunta, gaba daya sai ya amshe sauran kudin ya yi sha’aninsa da su. Gaba daya Afrah ta dorawa kanta hakuri da juriya gami da dangana. Ta maida hankalin ta wajen cigaba da yi masa addu’a tare da kauda kanta daga sa ma kanta muguwar damuwar da zata yi mata illa, komai a matsayin kaddararta take dauka a matsayin ta na musulma kuma tasan yarda da kaddara yana daga cikin cikar imanin musulmi.