Page 132
Tuntuni jarabawar Afrah ta fito ta kuma fita da sakamako mafi kyau, domin duk ta cinye ko pass daya bata da shi. Sai dai mafarkin ta na cigaba da karatu tana ganin kamar bazai tabbata ba, domin tana ganin abubuwa da dama sun canja dole wani abun sai tayi hakuri da shi. Yanzu abu biyu ta fi maida hankali a kai shine yi ma musaddik addu’a da kuma yi masa nasiha, gami da kokarin dawo da shi irin hanyar da ya baro a baya, domin cikama mahaifinta burinsa. Domin dai a kullum sai tayi tsayuwar dare, tana nema ma musaddik shiriya. Domin idan ka dauke wannan halin nasa bashi da wata makusa ko matsala, sai dai abu daya ke daure mata kai Shine a duk lokacin da take masa nasiha, ya kan nuna mata shi ma ba haka ya so ba. Duk abinda yake yi, ba a son ransa yake yin sa ba, To amma don me ya kasa yaki da zuciyarsa ya daina ya natsu? Wannan ita ce tambayar da kullum take neman amsarta.Ta bangaren Mallam Mahmud kuwa kullum ya samu haduwa da Afrah yana kara karfafa mata guiwa tare da yi mata addu"a. Hakan shi ne kadai ke sanyaya ran Afrah tare da karfata mata guiwar cigaba da zama da Musaddik cikin aminci.