Musabbabi Book 1

Page 133

by @yargidanimam

Zabe ya Gabato , hakan ya sa gaba daya Musaddik ko kwanan gida bai cika yi ba, sai ya kwana daya kwana biyu baya gida. Ran Afrah da hankalinta yana matukar tashi akan wannan bangar siyasar.bata so sam domin ta san hatsarn da ke ciki. tayi nasihar har ta gaji, amma Musaddik ya riga ya ya rufe kunnansa , sai dai a duk sanda ya kwana baya gida, idan ya dawo, ya kan dawo da kudi Domin har dubu biyar yana ba ta , ta rike ta ci abinci, a wannan tsakanin abinci baya yi mata wahala, duk abinda take so, shi take ci, da yake tana da hankali, ta kuma san samun na dan lokaci ne, ba me dorewa ba, shi ya sa idan ya bata takan kasa uku ta aje kashi biyu, ta ci abinci da kashi daya, da dan sauran hidimominta na yau da kullum, amma duk da haka Afrah babu farin-ciki a rayuwarta,kullum ji take yi kamar bangar siyasar nan zai iya kara jefa rayuwar cikin garari.

Alhaji Hamza Sarkin yakin kamfen din Haj. Hudah ne, wacce take neman takarar zama yar Majalisar Wakilai, ta Kasa.Yana zaune a katon falonta a gidanta na ganawa da manyan baki Gefe daya Musaddik ne a zaune yana karema falon kallo, yana nazarin yadda aka kawata falon da kayan alatu masu kyau da tsada.cikin kaguwa ya dubi Alhaji Hamza yace cikin yanayin maganarsa,

"Alhajin Allah, ni fa duk a rayuwata babu abinda na tsana irin jira, ina mutunta lokaci, shi ya sa ba na Kara lokaci akan wanda aka ba ni” Alhaj Hamza ya yi dan murmushi Yace “Mazaje ayi hakuri, na san hakan, batun yau ba