Page 134
itama Haj na tabbata akwai abinda ya tsayar da ita, amma na san tana hanya, bari na Kara kiranta” Ya tura hanmu a aljihunsa ya ciro waya, ya danna kenan, ya jiyo hon din motar Hajiya Hudah, ya yi murmushi gami da kallon Musaddik, a yayin da yake maida wayar cikin aljihunsa Yana cewa “Ga yar halak din nan ta iso”,Musaddik ya gyada kansa ya co "Ya dai kamala' Yana rufe dai kamata, amma ina dalili kayi ta zaman jiran mutum”, yana rufe bakinsa. Hajiya Hudah ta danno kanta cikin falon kyakyawar bafullatar mace ce, fara ce, amma ba inn farin nan me daukar ido ba, tana da kyawun fuska dai dai gwargwado hade da kyawun diri.Tana sanye da kaya na alfarma, kallo daya za ka yi mata, ka San goggaggiyar mace ce, wacce ta mallaki masu gidan rana, kuma wayayyiya wacce tasan abinda duniya take ciki. “Alh Hamza kuyi hakuri, na zaunar da ku ko? Kun san abubuwan da yawa ne, babu zama” 'Ta fada tana kokarin zaunawa. Alhaji Hamza muskuta ya gyara zamansa gami da yin dabi arsa ta murmushi ya ce
“Da girman kujerarki, barka da isowa Kada ki damu da hakan, ai dole ayi miki uziri” Ta amsa "Yauwa Alhaji", Ta fada 'tana kallon Musaddik, wanda yake zaune baida ko alamar gaisheta. Musaddik ya yi matukar yi mata kwarjini,haka nan kuma ta ji ya burgeta, yadda bai yi wani rawar jiki don ya ganta ba, da nuna baima damu da shigowar ta ta ba. Ta dawo da kallonta ga Alhaji Hamza wanda tun shigowarta ya kara samun nutsuwa ta ce. "Shine wannan wanda kace yana yi mana Kokarin nan?" Alhaja Hamza ya dube shi ya ce “Eh shine Haj Musaddik kenan, ku gaisa mana mazaje” ya fada yana sauke kallonsa a kan fuskar musaddik.