Page 135
Musaddik bai amsa ba, illa kallonta da ya ci-gaba da yi.sai daga bisani ya daga hannayensa biyu ya kai tsakiyar fuskarsa yace “Barka dai hajjaju”, tayi murmushi sosai tana kara kallonsa tace “ Barka dai, ina ta godiya dai”,ya girgiza kai yace “Ah kada ki damu, ai kin cancanci ayi miki komai saboda mu ma kina aikowa a sauke mana”. Dariya kawai tayi tana jin zuciyar ta na son ta dinga yabon musaddik da kuma jin komai ya yi yana burgeta. Alhaji Hamza ya fara magana. "Hajiya. Kamar yadda ki ka sani da wanda ba ki sani ba, amma na yi kokarin gaya miki Musaddik shine wanda yake mana kokan a wajen matasa, to kamar yadda na fara gaya miki a waya, ki ka kuma bukaci na taho da shi domin ku ga juna ku gaisa, Yan’uwan aikin nasa suna da bukatar Kudin kayan aiki, tunda zaben nan jibi ne, don haka suna bukatar kayan maye da makamai, wadanda za su sha a yayin tashin hankulan mutane a lokacin zabe, sai kuma kudade wadanda za su sa a cikin aljihunsu, domin jin karfin gudanar da aikin. Don haka a matsayinsa na ogansu wanda kuma da shi nake mu'amala, ba da su ba kuma duk jama'ar nan shine ya nemosu, shi ya sa suka wakilta shi akan komai.”
Hajiya Hudah ta gyara zamanta, gami da kara kallon Musaddik, wanda duk Kallon da za ta yi masa, ta kan sami zuciyarta da bugawa, yana kuma matukar kara yi mata Kwarjini tace *Musaddik ba dai matsala a can Bangaren naku ko?" Ya kara dubanta yana gyara zama yace *Matsalar kenan ta kudì da kayan maye, in dai da su, to za ku ga biyan bukata, ta bangaran mu, kuma jama"ar tawa korafi suke yi min suna ganin kamar ana yi min wata katuwar sauka ne ta tamaye amma bana aje musu nasu kason”.
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️