Musabbabi Book 1

Page 136

by @yargidanimam

Musaddik ya kara gyara zamansa ya cigaba da cewa “to a yadda na fahimce su, tunda ba mutunci gare su ba,suna Iya yi min bore a ranar zaben,su ki yi mana abinda ya kamata don haka sai ku san yadda za ku yi da mu idan kuna son komai ya tafi yadda ya kamata”.

Alhaji Hamza ya muskuta yana kallon Musaddik yace "Ba ku da sauran matsala, ga ka ga Hajiya Hudah nan, gani kuma a tsakiya,babu komai duk abinda ku ka nema, za ku samu” Hajiya Hudah ta dora kafa daya kan daya tana dan murmushi, yadda musaddik yake magana da kwanjinsa yana kara mata matukar kwarjini. Ta maida idonta kansa sosai tace “Babu damuwa, babu abinda zai gagara shi yasa kuma nace sarkin yaki ya taho min da kai,saboda duk abinda zai kawo mana cikas a cikin wannan tafiyar bama bukatar sa,muna son komai ya tafi yadda zukatanmu ke bukata”. Ta dauko katuwar jakarta da ke yashe a gefenta wanda da ita take yawo saboda jakar tana daukar makudan kudad,sannu a hankali ta bude jakar ta dakko naira dubu dari biyar ta mika ma Musaddik, yasa hannu ya amsa, ta maida bayanta ta kwantar a jikin kujerar sannan tace “wannan ka je ka raba masu, su sa a aljihunsu, domin su jidadin yi mana aiki”, Alhaji Hamza ya wage baki, yana mamaki. yana ganin duk mako gami da matsolancin Hajiya Hudah da tsoron fitar da kudinta, ta ba Musaddik duba dari biyar ba tare da ta ga jama'arsa ba. Wanda yasan ba ta taba yin hakan ga wani ba, tsarinta ne dole sai ta ga zahiri. In dai kudi za ta bayar, sai taga yawan jama’arka. Lalle Musaddik yau ya taki sa'a. Musaddik tunda ya karbi kudin yake juyasu ba tare da yace uffan ba, wanda ji Alh Hamza yake kamarya matse bakin Musaddik yasa shi ya dinga yi mata godiya akan komai, baya son wannan shurun da yake yi. Wanda hakan sam bai dami haj Hudah ba illama burgeta da yake yi. Domin kara janyo jakar ta yi ta fito da naira dubu dari hudu ta kara mika masa tace “wannan naka ne kai kadai”.

Cikin karin wani mamakin Alh Hamza ya zaro ido, zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tunanin wane irin matsayi musaddik ya samu a wajen uwar dakinsa.A yayin da Musaddik ya karba,lokaci daya a kuma Karo na farko Ya yi mata godiya, Ta yi murmushi tace “Wannan dubu dari biyar din kamar yadda na gaya maka, ka rarraba ma mutanen naka , na san a ciki zasu sami wanda zasu sayi kayan shaye-shayensu harma da wani biyan bukatar tasu,ni kawai burina a ranar duk akwatin da ku ka ga alamar ba zamu kai labari ba, to ku far masa, ko ku dauke shi ko ku