Musabbabi Book 1

Page 137

by @yargidanimam

Lalata shi. Idan kuma duk babu dama, to kawai ku tada fitina a wajen. Taimakon da na ke nema kenan a gare ku”.Musaddik ya ce "Kada ki damu, duk abinda ki ka lissafa za mu yi, sai dai wani hanzari ba gudu ba kuma” Ta ce "Ina jin ka". Ya ce "An dade ana amfani da mu a wannan harka, amma daga baya mu kan tura mota ne ta tashi, ta bulbulemu da hayaki,Ma'ana, da zarar kun sami biyan bukatar ku sai ku manta da mu, ku kyamace mu, a lokacin ne za ku san mu ba mutanen kirki bane, sai ku kulle yin duk wata alaka da mu, Wannan babban kuskure ne ku ke yi, domin muna yi maku abinda ko 'ya yanku bà su iya maku, don haka bai kamata ku dinga mantawa da mu ba bayan kun kafa gwannatin ku dare kan madafun iko”. Hajiya Hudah ta dubi Alhaji Hamza da har yanzu yake yi mata kallon mamaki, sannan ta yi murmushi tace,

"'Ka kwantar da hankalinka, za ka ga bambanci a wannan karon, domin in dai na haye wannan kujerar to da kai za'a tafi gwamnatin, kada ka Kara sa wannan matsalar a matsayin damuwarka, domin zan yi maganinta, da zarar na haye" Tun zamansa, sai yanzu ya saki jiki sosai domin ko banza ya jidadin maganarta yana kuma fatan ta cika alkawarin ta, yace "To godiya na ke ranki ya dade, Allah ya bamu nasara” daganan ya mike, yana kallon Alhaji Hamza yace “Alhajin Allah taso ka aje ni inda ka dauko ni"