Page 138
Yana magana yana dauko leda a aljihunsa, ya zuba duka kudin, ya daure. Alhaji Hamza ya ce "yanzu Kuwa zan maida kai”, Ya mike yana kallon Hajiya Hudah ya ce. "Gari fa ya yi zafi, ga abubuwa sun mika, jibi za'a fita fagen fama , ko zan sami na fetur?" Ta Yi masa wani irin kallo, gami da hade rai wanda tuni ganin hakan yasa ya cire ran zai samu wani abu a hannunta,amma Alhaji Hamza bai san irin tunanin da ta yi ba, bayan ta dubi Musaddik, sai ta janyo jakarta ta Kirga dubu talatin, ta mika masa. Ba yabo, ba fallasa ya karba, yanzun nan ta ba musaddik naira dubu dari hudu. Amma shi da kullum yake wahala akan lamarinta. Ta kirgo dubu talatin ta ba shi, ba tare da godiya ba ya ce "Mun barki lafiya' Tare suka jera da Musaddik suka fice, yayin da Hajiya Hudah ta bi su da kallo har suka bace ma ganinta. A zahiri ta ji dadin haduwa da Musaddik,domin ya yi mata matukar Kyau kuma bai yi kama da irin iskancin da Alhaji Hamza yake kira masa ba, domin bata dauka zata same shi da sauran nutsuwa ba. Sosai taji zuciyar ta ta aminta da yin hulda da shi ba tare da wata fargaba ba
Alhaji Hamza kuwa suna fara tafiya, ya a mota ya waiwayo ya dubi musaddik Yace “Gaskiya ban san irin sa'arka ba Mazaje” Ya dan dube shi ya ce "Na me fa?" Ya ce "Na yadda Hajiya Hudah ta ba ka Wadannan makudan kudin ba tare da ta ga jama 'ar da za ka raba ma ba, ta yarda da kai cikin kankanin lokaci.wanda ba dabi’ar ta bace yin sabo ko damka ma wani amanarta nan da nan,don ko ni da na yi shekara da shekaru tare da ita, idan maganar kudi ta zo to fa sai ta ga komai da idonta, duk da tana haukar son wannan kujerar, za ta iya yin komai, domin hawa kujerar.