Musabbabi Book 1

Page 139

by @yargidanimam

To fa duk da haka, ba ta kwasar kudinta irin haka tana bayarwa. Sai ta ji, ta kuma gani. Shi ya sa yadda ta ba ka wannan kudin abin ya yi matukar ba ni mamaki, Don mace ce me son abin duniya”. Musaddik ya yi murmushi ya ce “To ai komai ya zo gaf ne Kila ta yi tunanin idan ba ta bada kudin ba, za su yi boren ne, kamar yadda na gaya mata,tunda kuma tana son kujerar ai babu abinda ba zata yi ba gudun kada a sami matsala,kuma kaga ba mu taba haduwa da ita ba sai yau”. Alhaji Hamza ya nunfasa ya ce. "Allah shi ya san dalilinta na yin hakan, sai kuma ita kanta, ka na ji?" Ya juyo ya kalle shi ya ce. "Ina jin ka ya akayi Alhajin Allah “

Alh Hamza yace 'Dan yago min wani abu, don wannan dan kudin da ta ba ni, ba abinda za su yi min, ina da dumbin matsaloli amma ta hadani da dubu talatin, saboda tsabar rashin adalci”. Ba tare da yace komai ba Musaddik ya bude ledar, ya dauko dubu dari biyu cikin kudin da ta ba shi, ya mika masa. A gaggauce Alhaji Hamza ya ce "Dubu dari biyu ne fa mazaje”.

Ya gyada kai ya ce. "Ina sane, Wadannan sun isa mu raba ko dubu biyar-biyar ne, ba damuwa, sauran dubu dari biyun nawa zan karama mutanena akan nasu duk sai mu raba saboda nasan kai ba za ka kashesu ta hanyar da za mu kashe ba, za ka yi amfani da su a inda ya dace ne, tunda kai ka ji dadi ka mori rayuwarka, babu shashanci a ciki. Idan na tafi da kudin nan, ni a banza zan kashesu akan abinda ba zai taba amfanar rayuwata ba”. Cike da tausayinsa. Alhaji Hamza ya ce “Mazaje iyalinka fa?"ya girgiza kai Yace "Ko na kai mata, sai ta tuhume ni ina na samo su, bata son wannan bangar siyasar da nake yi, kai mata kudin ba zai faranta ranta ba, sai dai ya bakanta ranta, ni kuma a duniya babu abinda na tsana sama da bacin ranta. Inda ina da iko da kaina da duk abinda nake yi yake bata mata rai na daina, to na zama tamkar wanda ake sawa yin abu dole idan banyi ba bana jindadi, kuma ko ma na kai mata kudin ta amsa to ni ne zan koma na kara karbesu na kashesu a banza, a duk sanda kuma na je amsa, ranta sai ya baci, domin ta