Musabbabi Book 1

Page 140

by @yargidanimam

san abinda zan yi da su, amma ba za ta taba nuna min bacin ranta ba, za ta dauka ta ba ni, to kaga gara ma kada na kai mata." Alhaji Hamza a sanyaye ya karbi kudin hakika halin Musaddik, ba irin halin da Yake kallonsa da shi ba ne da kuma wanda yake aikatawa ba , kwarai yana da kyan zuciya, tausayi da kuma imaninsa, wannan halin da yake ciki hakika ba nasa bane, bai kuma dace da shi ba, ga kwarjini da dadin mu'amala. Karo na farko kenan da Alh Hamza ya fara yi masa addu' ar shiriya. Ya kirga dubu ashirin ya mika masa yace. "Ga shi ka kai ma matarka, na tabbatar kafin ka waiwayesu, sun kare, tunda babu yawa, kuma ba zata tuhumeka da inda ka samo su ba sabida basu da yawa kamar yadda na fada,don Allah ka kai mata”. Ba tare da musu ba, ya karba, ya tura a'aljihunsa har suka kai inda ya aje shi. Alhaji Hamza fatan shiriya yake masa, tare da yi masa addu'a, ya kuma sa a ransa ba zai taba mantawa da abinda Musaddik ya yi masa ba a rayuwa, tare kuma da alkawarin sa shi a cikin addu'arsa, a duk sallolinsa na farilla. A daran ranar da wuri Musaddik ya koma gida, hakan ya faranta ran Afrah, ta kawo masa abinci ya ci ya koshi. Tabbas yana jin dadin abincin matarsa, ba tun yau ba, domin ta iya girki.Afrah Ta kai, ta dawo yana kallonta, haka nan yake jin kunyarta, a duk lokacin da take hidima da shi Lokaci daya kuma tausayin ta yana kara kama shi.

Yar gidan imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM