Page 141
Cikin wata irin daskararriyar murya musaddik yace “Zo nan ki zauna” ya fada yana nuna gefensa da hannunsa. Afrah ta koma a hankali ta zauna, tana kallonsa ya ce, yana cigaba da kallonta "Zauna haka nan ki huta ma kanki, nagode Kwarai da gaske, yadda kike kulawa da ni idan ina tare da ke har gani nake ban kai ki ba ni irin wannan cancantar ba, sai na dinga jin ta ko wane bangare na gaza a kanki”
Ta dan yi murmushi,tana kara gyara zamanta ta ce “Haba yaya Musaddik, wai sai ka dinga yi min godiya akan abinda ya kamata na yi maka?bayan hakkinka ne nayi maka komai, batun cancanta kuma Allah ne ya baka wannan cancantar a matsayin ka na shugaba a gare ni” ido ya dora mata sosai yana jin tana kara burge shi yana jin wani irin shauki a kanta. Yana da kima da martaba a cikin gidansa Afrah bata taba kyamatarsa ba, yana jin zai iya yi ma Afrah komai domin ta jidadi ta kuma samu kwanciyar hankali,to amma me yasa ya kasa daina abinda yake yi wanda acikin abinda zai iya yi mata din wannan shine karami, amma me yasa ya kasa.ya sauke numfashi a hankali
Yace "Na sani, duk da haka dai na gode, domin ni kadai nasan irin kokarin da kike yi a kaina, Allah ya kara yin albarka a cikin rayuwarki kanwata”. Ta jidadin furucinsa tayi murmushi tace “Amin” a ranta kuma addu’a take masa Allah ya kawo karshen al’amarin sa. Musaddik ya ciro dubu ashirin a aljihunsa, ya mika mata, ta sa hannu ta karba cike da mamaki tana kallonsa.tace “Na meye wannan kudin?” Yace “Na ki ne, wani abokin harkar siyasata ne ya ba ni, ya ce in kawo miki" ta yi dan murmushi tace “Amma nagode Allah ya saka masa da alheri,to amma sai ka dauka duka ka ba ni, ka diba mana”, Ya girgiza kai ya ce "A'a na ki ne, ba zan dauki ko sisi ba” Za ta yi magana kenan, ya mike yana gyara kwalar rigarsa yace “Ni zan fita" Nan da nan Afrah ta gintse fara'ar fuskarta gami da marairaice murya tace “Ina kuma za ka tafi?"ya dan dakata yana kallon yanayinta, yana jin wani abu wanda ada baya ji a game da Afrah, domin a yanzu ko yaya ta canja fuska ko ta nuna damuwarta akan wani abu da zai aikata yakan ji tamkar an dora masa dala da gauron dutse a kansa. Yanzu ma hakance ta kasance da shi. A hankali ya koma ya zauna daf da ita yadda suna jin bugun zuciyar juna, nan dan Afrah ta ji wata kasala ta rufeta, ta yi saurin yin kasa da idanunta. Ya mika hannunsa ya janyo hannunta ya fara nurzasu shi kansa jinsa ya yi yana neman fadawa wani hali, wanda baisa ya saki hannun nata ba, a sanyaye ya kira sunanta “Afrah”, bata iya amsawa ba illa idonta data dora masa. Ya cigaba da cewa “ki yi hakuri, a wannan gabar dole sai kin kara hakuri akan wanda ki ke yi da, zabe ya zo na kuma riga nasa kaina a cikin wannan aikin, dole ina bukatar hadin kanki, kamar yadda ki ke bani a ko wane lokaci”.
Afrah ta lumshe idanunta ta bude ta kara dorasu akan fuskar nijinta, tayi dan murmushi tace “Ba ni da ikon shiryar da wanda Allah ya batar sabida haka nasan bani da ikon da zan dorawa kaina damuwar abinda yafi karfina, shi yasa nake yi maka addu’a a kullum, ina kuma da tabbacin wata rana Allah zai share min kukana,sai dai ba zan gaji da rokonka ba, don Allah Yaya, don girmansa da kuma darajarsa, ka yi ma kanka fada, ka natsu, ka san rayuwar da ka ke yi, ba ta dace da kai ba. Ka yi ma kanka fada, tun kafin ka fara haihuwa, a fara goranta ma yayanka” Musaddik ya kankame hannunta ya dora su duka akan fuskarsa, yace “ina rokon Allah kada ya dauki raina ba tare da burinki ya cika a kaina ba”. Ta kasa jurewa gaba daya kawai saita rungume musaddik tsam a kirjinta shi ma tamkar ya na jira ne don haka shima sosai ya rungumeta ya na shinshinar kamshin jikinta, lokaci daya kuma dukansu suka yi ta kuka me motsa zuciyar duk wani mai saurare. Basu san iya lokacin da suka dauka suna kuka ba, sai daga bisani Musaddik ya janye jikinsa daker tashi kawai ya yi ya kalleta, ba tare da Yace komai ba, ya fice, daga dakin, a hankali ta gyara zamanta a kan kujerar.