Musabbabi Book 1

Page 142

by @yargidanimam

hawaye na cigaba da malala mata, alokacin da ko wane magidanci yake dawowa gidansa, shi a lokacin yake fita shin yaushe musaddik zai fahimci masifar da yake ciki, yaushe kuma zai gane girma a kullum zuwa masa yake .hankali ta daga hannunta sama tana addu'ar neman shiriya ga mijinta

A ranar sai tsakar dare Musaddik ya dawo gidan, tana sallar nafila ya dawo cikin maye,don haka ko ta kanta bai bi ba, ya wuce ya yi kwanciyarsa da takalmi a kafarsa. Sai da ta idar da addu'o' inta ta zo kwanciya, sannan ta cire masa takalman. Amma irin warin da Musaddik yake yi, ya hanata kwanciya kusa da shi,duk da tun dazu take jinta cikin matukar sha’awar mijinta. sai falo ta dawo ta kwanta akan kujera, tana zubar da hawaye, Bakinta na fadin lahaula wala kuwwata illa billah, domin sanin wannan addu’ar tana da matukar tasiri wajen korar dukkan damuwa. Kullum Musaddik bata mata rai yake yi da dabi'o' insa, amma har yanzu zuciyarta ta kasa tsanarsa, maimakon haka ma tausayinsa ya fara haifar mata da kaunarsa, don yadda take jin Musaddik yanzu a ranta tasan tana sonsa domin tabbas ba don wannan halin ba. Musaddik mutum ne. kuma miji ne da ko wace mace zata so samunsa a matsayin miji.

Tun safiyar ranar da za'a gudanar da zaben, Afrah ta sami kanta da matukar faduwar gaba da kuma damuwa, domin gaba daya ba ta gamsu da yanayin da mijinta ya fita ba, don haka bakinta ya kasance cikin addu’a,