Page 143
Ta bangaren Musaddik kuwa, yana can tare da mukarrabansa suna bin mazaba-mazaba suna aikata abinda aka umarcesu da aikatawa, inda suka ga Hajiya Hudah za ta ci. Su kan daga ma wajan kafa, inda ko ba za ta ci ba, da sun ga alamar haka, to su kan tada fitina a wajen. Ta hanyar dukan mutane da kuma kone - kone, a yayin da duk bayan mintuna Alhaji Hamza da Hajiya Hudah suna buga masa waya, domin jin halin da ake ciki. Abu ya kai makura fitina ta yi kamari , domin har an fara rasa rayuka . Jama"a sai gudu suke yi. Domin tsira da rayukansu. Nan da nan Kafin ka ce meye wannan? "Yan sanda sun cika duk wajen da akwai matsala. Haka nan suka shiga kama jama'ar wajen a Kokarin su na kawo karshen fitinar, cikin wadanda aka kama kuwa har da Musaddik da kuma wasu tsirarun abokan aikinsa. Wannan kamun ko a kwalar rigar Musaddik, domin dai ya san yana da wadanda za su fito da shi, don ya san Alhaji Hamza ba zai taba barinsa a hannun Yan sanda ba, don an yi hakan ya fi a kirga. Tunda ya dade yana aiki da Alh Hamza ko ba’a kan siyasa ba.
Tunda Afrah ta fahimci fada ake yi, domin yadda garin ya yi shiru, sai warin tayoyin da ake konawa; ka na daga cikin gida ka na hango inda wuta ke tashi, tana rimi, tuni hankalin Afrah ya yi mummunan tashi, fatanta daya. Allah ya sa fitinar ba ta rutsa da Musaddik ba. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye damuwa ta kusa kaita kasa.