Page 144
A yayin da ta kira wayarsa ya fi sau a kirga amma wayar na kashe, tun daga lokacin hankalinta ya kara tashi, har dare ba Musaddik, ba alamarsa , duk da a lokacin gaba daya abubuwa duk sun lafa, da taimakon Jami’an tsaro komai ya dawo dai-dai. Tana ganin zuwa lokacin ya kamata ace Musaddik ya dawo gida. Amma har gari ya waye, bai dawo gida ba.Zuwa yamma damuwar Afrah ta Kara fadada, ta kasa ci ko sha. a daddafe gari ya Kara wayewa, kwana biyu kenan babu duriyar mijinta, tasan yakan kwana baya gida amma wannan karon tana ji a jikinta ba lafiya ba.hakurinta da dauriyarta sun kare don haka ta fito daga bangarenta zuwa bangaren Haj kilishi. kai tsaye falon Hajiya Kilishi ta nufa. Ta tadda ita tare da Hajiya Rakiya suna zaune suna hirar hatsaniyar da ta faru shekaranjiya. Yadda Afrah ta fado falon a gigice, ya sa Hajiya Kilishi ta waigo ta dubeta a firgice, tana ganin itace ta canja fuska tace “ke lafiya zaki fado ma mutane falo haka, menene?” Afrah ta dakata tana kokarin mallakar nutsuwarta, zuciyar ta kuma tana tunatar da ita alwashin da ta ci na cewa ba zata nemi taimakon haj kilishi akan komai ba, sai dai kuma wata zuciyar tana gaya masa ba bu abinda ba zata yi ba saboda musaddik, don haka tace cikin sanyin murya, "Ki yi hakuri Hajiya. Ina cikin matsala ne, na san kuma za ki iya taimakawa, shi yasa na zo gare ki” Haj Kilishi ta dubi Hajiya Rakiya da take yatsina fuska ta ce “Me yafaru?” Afrah ta dan gyara tsayuwarta, sannan tace "Hajiya, tun shekaranjiya da Yaya Musaddik ya fita wajen zabe bai dawo gida ba, shine na ke cikin fargabar ko hargitsin daya faru ya rutsa da shi ne, saboda wayarsa tana kulle bata shiga”
''To shi ne ki ka zo guna na yi maki me?"Cewar Hajiya Kilishi. Cikin isa da gadara. Duk da naganar ba ta ma Afrah dadi ba, bai hanata kara