Musabbabi Book 1

Page 145

by @yargidanimam

marairaice murya ba tace "Shine na zo ki taimaka min,kisa hannu tunda hannu daya baya iya daukar jinka, ki tayani binciken inda yake, tunda nasan kina da hanyoyin da zaki iya sanin inda yake”. Cikin fusatar da Afrah ta rasa dalili Haj kilishi tace,

"Tunda ni gidan Rediyo ce ko? Ko gidan jarida , Ina ruwana da rashin dawowarsa gida, kuma ke akan lamarin Musaddik, ai kin wuce hannu daya, hannu miliyan ce, meye na karaya Kuma yau ba kin ce kin ji, kin gani ba. Kuma banda ma iya yi da neman magana irin naki, da kuma kokarin dora min wahala yau Musaddik ya fara fita ya je ya kwana bai dawo gida ba? Dan iska har wani damuwa za ayi da halin da yake ci, bayan kowa yasan yana can wajen iskancinsa hankali kwance”, Hajiya Rakiya ta yi tsaki ta ce "Ni ba Karamin firgita ni ta yi ba, meye wani Musaddik da za ki tashi hankalinki, don kawai bai dawo gida ba, sai kace yau ya saba. Don Allah ki sassautawa kanki wannan wahalar tun kafin ki kai ga faduwa”. Haj kilishi tace “To ai ni ban ma gane hausar wai na taya ki binciko inda yake ba, to ni ina da abin yi, ba zaman banza na ke yi ba, balle ki ce kin ga ina zaman banza ne, ki ka ba ni aikin yi. Musaddik Allah ya dawo miki da shi lafiya, amma ni babu abinda zan iya yi miki." Afrah da take tsaye, zafin maganganun su Hajiya Kilishi ya tilasta ma idanunta fitar da wasu zafafan hawaye. Zuciyarta tuni ta cika da badama da danasanin kawo kanta wajen Haj kilishi don ba don ta kawo kanta ba babu yadda za’ayi su kara mata bakinciki a kan wanda take ciki.Hajiya Kilishi ta juya gun Hajiya Rakiya suka ci-gaba da maganganunsu, suka bar ta nan tsaye, tamkar babu wata halitta a cikin falon bayan su.

Yar gidan imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM