Page 146
Ahankali Afrah tana goge hawayenta, ta fito daga falon, wanda lokaci daya Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka barke da dariya, me cike da wulakanci.Hakan ko ba karamin Kara Kona ran Afrah ya yi ba.A daddafe Tana shiga daki ta fada kan kujera ta cigaba da kuka me motsa zuciya, daga bisani, ta tabbatar kukan bazai amfaneta da komai ba , don haka ta tashi ta wanke fuskarta, ta dakko hijabinta ta zura, ta daura nikaf dinta, ta fito dai-dai kofar get ta hadu da Baba Maigadi.Ganin yanayinta. Ya tilasta masa yi mata magana, domin Baba Mai-gadi ya damu da lamarin Musaddik kwarai da gaske,domin tun kafin a haifi Musaddik yake gadi a gidan har zuwa yanzu da tsufa ya kama shi, duk irin rayuwar da Musaddik ya shiga, ya sani, yana daya daga cikin masu masa addu'a, masu kuma damuwa da lamarinsa. "Lafiya dai ko Afrah, za ki fita cikin ranar nan?" Afrah ta dan daidaita muryarta tana kokarin boye damuwarta tace “Baba fitar ni ma ta dole ce, ba ka lura ba yau kwanan Yaya Musaddik biyu, bai dawo gida ba, kuma wayarsa tana kashe”,Ya jinjina kai cikin damuwa sosai yace "Na sani Afrah, domin har wayarsa na Kira ni ma domin naji inda yake, amma ni ma a kashe nake jinta a duk likacin da na kira, na shiga damuwar ko hatsaniyar da aka danyi na siyasar nan shekaranjiya ta rutsa da shi be”.Afrah tace “Dama ni ma fargabata daya ce irin taka , kada ace ya fada cikin hayaniyar, hankalina ya tashi matuka domin bansan a wane hali yake ciki ba” Ya ce "Dole ki damu, to yanzu menene mafita? Ya zamuyi mu san yana wane hali ne”, Afrah ta rausayar da kai tace “Eh to na bukaci Haj ta taimaka tasa hannu tunda tana da hanyoyi amma ta nuna ba zata iya taimaka min ba