Musabbabi Book 1

Page 147

by @yargidanimam

don haka yanzu na fito zan je na dudduba (Police Station) mafi kusa ko zan dace da sanin halinda yake ciki” Tausayi da sha'awar halayenta suka kama Baba maigadi ya gyara tsaiwarsa yace “Allah ya yi miki albarka, amma ke ma ai kin san Hajiya ba za ta taimaka miki da komai ba akan Musaddik. Allah dai ya takaita wahala yasa baya cikin wata masifar , ni ba don kada na sami matsala da haj ba, ai da na tafì tare da ke mun neme shi ko Allah zaisa mu dace” Ta girgiza kai tace “A'a Baba kada na ja maka matsala, ka zauna kawai abin ka, zanje ni kadai, na gode da kulawarka”. tana gama fadan haka Ta juya ta fice da sauri A yayin da ya bita da kallon tausayi, tunda yake bai taba ganin muguwar mata irin Haj Kilishi ba, ta maida dan kishiya marayan Allah, ya zama abokin gabanta, ta sa shi a ranta, me yasa mata suke maida dan kishiya abokin gabansu ne?bayan shi da na kowa ne, domin baka san wa zai more shi ba, babu ruwan yaya da kishin da ke tsakanin iyayensu.batun yau ba zuciyarsa bata yi masa dadi akan yadda Haj kilishi ke tafiyar da rayuwar musaddik, kamar yadda dabi’unsa na yanzu suke tayar masa da hankali. Domin har yanzu ya kasa yarda da cewa gata ne ya maida Musaddik haka.

Akalla fitar Afrah ta je (Police Station) kusan hudu, tana cigiyar Musaddik, amma ba ta same shi ba ba ta kuma sami labari a kansa ba. Ko kadan bata son tayar ma da mahaifinta hankali kamar yadda nata ya tashi shi yasa bata son ta gaya masa halinda ake ciki, amma dole yasa ta ga sai ya sani domin tasan duk duniya bata da wani mataimaki bayan mahaifinta.Ana kiran sallar magariba ta isa gidansu. A kofar gida ta tadda Malam Mahmud yana alwala, ta tsaya har ya idar da alwalar. A cikin damuwa ya dubeta, domin jikinsa ya gama gaya masa ba lafiya, ya dubeta a sanyaye yace “shiga cikin gidan, ki yi sallah, zan je masallaci, idan na fito zan same ki”, Cikin dishewar murya Afrah tace