Musabbabi Book 1

Page 148

by @yargidanimam

"To, a dawo lafiya." Sannan ta shiga gidan.Mama Hauwa na kwasar tuwo. Na'ima na zaune kan tabarma a kofar dakin Mama Hauwa Tana shigowa. Mama Hauwa ta katse fara' ar fuskarta, ta yi kicin-kicin da rai daker take amsa gaisuwarta, ganin hakan ya sa ta koma kan kujera 'yar tsugunno a kofar dakin mahaifinta ta zauna cike da damuwa, ba daman ta yi sallah, tunda yau ta tashi da fashin sallah.sai dai bakinta baya rabo da ambaton Allah wato zikiri.

Bakin Mama bai bude ta tambayeta dalilin zuwanta gida a wanna lokacin da ba ta saba zuwa ba, wanda da yar da ta haifa ce da tuni tabar duk abinda take yi ta dawo gareta domin ta ji dalilin zuwanta. kamar yadda Na'ima ko magana ba ta yi mata ba. Ka'idar Malam Mahmud sai ya yi sallar Issha'i, sannan yake dawowa gida, amma yau ana idar da sallar magariba ko addu'a bai tsaya yi ba, saboda ya matsu ya ji damuwar *yarsa, ya dawo gida Ya bukaci a shimfida masa tabarma. Mama Hauwa ta dube shi tace

"Hmmm Ka dawo da wuri ko a kawo tuwon yanzu?" Ya dubi Afrah ya ce "Eh, na dawo ne, saboda Afrah, bar abincin sai anjima" Mama Hauwa ta tabe baki, ba tare da tace uffan ba. Ya Kara kallon Afrah, sannan ya ce “Afrah kin ci abinci ne?" Ta girgiza, kai alamar ba ta ci ba. Agaggauce ya kwala ma Mama Hauwa kira, wacce tuni tabar wajen, ta amsa gami da tahowa, ya dubeta ya ce "Ki ba Afrah abinci ta ci”. Ta yi mata wani irin kallo ta ce "Oh cewa ki ka yi ban ba ki abinci ba?" Ta yi saurin girgiza kai ta ce. "A'a ban ce masa komai ba, tambayata kawai ya yi na bashi amsa”, ta fadi maganar cikin nuna alamun rashin son yin hayaniya, mama Hauwa Ta saki tsaki ta ce