Page 149
“Idan ma kin gaya masa ban baki abinci ba , wannan matsalar ki ce, tuwo na ban sa da ke ba, san da ki ka shigo kuma na riga na gama kwasa, tunda ban san za ki zo ba, to nawa ki ke so na dauka na baki, hamshakiya “ Malam Mahmud ya ce a fusace "Ki ba ta nawa ta ci”, Afrah ta gurgiza kai da sauri tace “A’a Baba ni bana jin yunwa a koshe na ke". Mama Hauwa tayi saurin cewa “To ka ji, a koshe take” .Ya yi mata wani mummunan kallo yace "Na ce ki dauko min abincina ko”
Ganin fusatar dake kan fuskarsa yasa Ta juya itama a fusace tana fadin "Kai ka sani, ina ruwana cikinka nefa, ba nawa ba. Ke Na’ima dauko abincinsa ki kai masa” Tana gama fadin haka, ta shige dakinta, Yayin da Na’ima ta dauki abincin ta je ta kai masa, ita ma tana ajewa ta shige daki. A hankali Afrah ta goge hawayen da ke fita mata a ido. Rana zafi, inuwa kuna. Malam Mahmud ya tabbatar mata ba Zai saurareta ba, har sai ta ci abinci ta koshi, hakan shi ya tilasata mata cin tuwon, tana ci, amma tamkar tana cin guba ne, domin babu abin da ke mata dadi a bakinta. Sai bayan da ta kammala, sannan ya bukaci jin abinda ya kawota gida a cikin wannan daren, duk da zuciyarsa ta gama gaya masa matsalar musaddik ce
A hankali Afrah ta gaya masa komai. Ta kara da cewa “bayan fitowa ta gida na je (Police Station) har guda hudu, amma ban same shi ba, shine na ga ya dace na zo na gaya maka tunda ban da wanda zai taimaka min sai kai”