Page 150
Damuwar Malam Mahmud ta Kara yawa Ya gyara zama yana lissafin ta inda zai fara lokaci daya yana cewa “Daman Haj kilishi ai ba za ta iya taimakawa akan abinda ya shafi Musaddik ba, kema da gangan ki ka bukaci taimakonta amma kada ki damu, ki kwantar da hankalinki, da ikon Allah babu abinda zai same shi, zai Kuma dawo gida cikin Koshin lafiya” Karo na farko kenan da ta ji ta sami saukin damuwa domin duk addu’ar da mahaifinta zaiyi mata tasan karbabbiya ce a wajen Allah.Ta ce "Allah ya tabbatar da hakan Baba, yace "Yanzu dare ya yi babu inda zan fita nemansa amma Ni da kaina gobe zan fita nemansa, za' a kuma dace in sha Allah domin banji a raina wani mummunan abu ya same shi ba, kema kuma ki sassauta ma kanki damuwa” Ya Kara kallonta cikin matukar so da tausayi , ya ce "Tashi na maida ke dakin mijinki" tace “Toh". Daga nan ta mike, za ta je dakin Mama Hauwa, domin ta yi mata sallama, Malam mahmud ya dakatar da ita ya ce. "Ba sai kin mata sallama ba, wuce mu tafi”. Ba tare da musu ba, ta juyo suka tafi baki dayansu cikin damuwa.
Yar gidan Imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️