Page 151
Ta bangaren su Hajiyn Hudah kuwa, tunda aka sanar da sakamakon zabe, suke cikin matukar farinciki mara misaltuwa, a dalilin lashe kujerar ta da ta yi, duk burinta ya gama cika.sun kasa zaune sun kasa tsaye, saboda tsananin murna sai karbar waya suke daga ko'ina, domin taya su murna. Amma duk da haka hankalin Hajiya Hudah yana wajen Musaddik, ta kasa sukuni tana matukar son ta san halin da yake ciki.Daga bisani ta samu kebewa da Alhaji Hamza, domin su tattauna, "Alhaji Hamza har yanzu ba wani labari a game da (Police Station) din da aka kai Musaddik ne?" Alh Hamza ya dan jinjina kai ya ce. “Kokarin da na ke ta yi kenan, amma har yanzu ba'a gano min Police Station) din ba, amma mutane hudu nasa su bincika min Kuma duk suna da himma nasan zasu iya nemo mana inda yake, na san za' a dace" Hajiya Hudah ta numfasa cike da damuwa tace “Ban san dalilin daya sa farin-ciki na yake raguwa ba, a duk lokacin da na tuna ba mu san halin da Musaddik Yake ciki ba, don Allah Alhaji Hamza ka yi iya okarinka, domin gano halin da yake ciki, yau Kwanaki biyu kenan fa ba wani labari. Alhaji Hamza cike da mamakin yadda ya ga ta damu akan Musaddik, matar da ya san halinta na rashin nuna damuwa akan rayuwar kowa, sai ta ta rayuwar, amma yau ji yadda duk ta gigice ta fita hayyacinta duk murnar da take ciki bata taka rawa ba wajen dakushe damuwar da take ciki ba a game da Musaddik, shin wane irin matsayi Musaddik yake da shi a wajen uwar dakinsa. Alh Hamza ya hadiye mamakinsa gami da kallonta yace “zanyi iya kokarina in sha Allah mu gano inda yake mu kuma fito da shi, tunda mun sami tabbacin yana daya daga cikin wadannan jami’an tsaro suka kama”. Haj Hudah ta numfasa tace “ Amma dai kana ganin ba zai bude baki ya fadi sunan mu bq a gaban yansanda”. Ya yi saurin girgiza kai yace “ wa musaddik ai ban taba ganin me amanarsa ba a cikin irin masu halin sa, ai da ya fadi sunan mu a gare shi gara an kashe shi,” ta lumshe manyan idanunta ta bude zuciyarta ta kara cika da sha’awar musaddik ta kara ji a ranta lalle wannan abokin tafiya ne.