Musabbabi Book 1

Page 152

by @yargidanimam

Don haka ta kara gyara zamanta tace “Alhamdulillah to don Allah kayi iya yinka, domin , ba na son tun Yanzu ya fara tunanin ba shi da amfani a gurin mu ya dauka bamu damu da nemansa ba” Alh Hamza yace “ Babu damuwa, komai zai tafi yadda yakamata” Ta gyada kai ta ce "To godiya na ke sarkin yaki, ko nawa aka nema idan an ganshi zan bayar domin a fito da shi” Alh Hamza ya yi dan murmushi yace “Na sani tabbas zaki iya ba da ko nawa ne domin hakan ya tabbata “, bata ce komai ba, ya kara gyara zamansa yace

“Ya shirye-shiryen party da za ki gudanar zai kasance?" Ta girgiza kai ta ce. "Batun Musaddik da gano inda yake, ya fi komai muhimmanci a yanzu ni a guna, saboda haka ba maganar Party har sai an san halin da yake ciki." Nan ma zuciyar Alhaji Hamza ta cika da mamaki irin wannan karbuwa daya samu cikin kankanin lokaci daga uwar dakinsa, abinda har yanzu ya kasa gasgatawa , ya gyada kai yace "Hakan yana da kyau. Allah ya nuna mana shi, ya takaita masa wahala” Ta amsa da "Amin". Dai-dai lokacin wayar Alhaji Hamza ta dauki kara da karfi, da sauri ya dauka, ganin daya daga cikin yaran daya sa su nemo masa Musaddik ne. Watau Isah. Daga daya bangaren Isah ya amsa “Alhaji mun gano (Police Station) din da aka kai musaddik(Police Station) din Kan Tudu ne, amma abinda me kulawa da su ya fada, shi ne zuwa gobe za’a' a wuce da su Abuja" Alhaji Hamza ya zaro ido”Abin har yayi Kamari haka ,Abuja kuma?" Ya amsa “Kwarai da gaske”Ya ce "To na gode, sai mun hadu."