Musabbabi Book 1

Page 153

by @yargidanimam

Yana aje wayar ya juya ya dubi Hajiya, Hudah wacce ta tsare shi da ido duk ta kosa ya gama wayar ta ji abinda ake ciki tace “Me yake gaya maka ne?”Alhaji Hamza yace “Yana (Police Station) din Kan Tudu, kuma gobe za'a wuce da su Abuja don haka sai mu san abin yi, na san dai za mu kashe kudi masu yawa kafin fitowarsa”Haj Hudah tace "Ko nawa ne, na gaya maka zan iya Kashewa domin ya fito, tunda koma wane hali ya shiga ai akan aikin mu ne, kuma mu ne dalili, saboda haka ya kamata ka zo ka tafi asan abin yi".Alhaji Hamza ya dubi agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa, karfe goma sha daya saura kwata ne na dare Yace “Eh dole yanzu ya kamata na tafi tunda goben ne suke tunanin kai su Abujan”.

Hajiya Hudah ta wuce zuwa cikin dakinta ta dakko kudi har nera dubu dubu dari uku , ta mika ma Alhaji Hamza ta ce. "Ka rike wannan, ka je ka ji yadda za’ayi da yansandan, duk yadda za’ayi ayi domin ganin an cire sunansa a cikin ko wace takarda dake police station din”. Da sauri Alh Hamza ya karbi kudin, Lokaci daya ya fice a hanzarce.

Zuwan Alhaji Hamza (Police Station) din a kalla sai da ya sami ganawa da 'Yan sanda guda shida, sannan ya samu nasarar samun Insifektan da Matsalar ke hannunsa, lamarin ya zama na sirri,domin matsalar ta su Musaddik me girma ce.suna tsare ne a matsayin yan ta’adda wadanda ake amfani da su a lokacin zabe domin a tada hankulan jama’a, da kuma ana tuhumar su da laifin lalata akwatin zabe da kuma sacewa, sai dai har yanzu sun ki fadar wanda su ke ma aiki.