Musabbabi Book 1

Page 154

by @yargidanimam

A dalilin kuma sun ki fadan wanda suke ma aikin, ya sa matsalar tasu ta kara girmama, shi ne dalilin ma da za’a maida su Abuja. Wata Kila a can idan su su ka ga ba Sarki sai Allah sa yi bayani.domin acan din ana iya batar da su har abada . To zuwan Alhaji Hamza dai, shine ya Ceci Musaddik da sauran yaransa, domin da kyar Insifektan ya yi alkawarin goge matsalar tare da bada belinsu, amma sai da suka yi ciniki. Yi cinki saboda tsabar cin hanci da rashawa ya yi ma kasar mu illa.Domin shi ma ya ce sai ya sallami yaransa ya rufe masu baki, don kada ta tashi a wajen manyansu. Don haka Naira dubu dari shida Insifektan ya nema. Haka aka yi ta ciniki har kudin suka koma dubu dari biyar . Don haka Alhaji Hamza ya ba- shi dubu dari biyu da rokon zai dawo gobe ya cikasa masa dubu dari uku, Amma Insfektan bai yarda ba, har sai da ya hada shi da Hajiya Hüdah a waya, suka yi magana, ya tabbatar ita ce, sannan ya amince. amma ba su yi maganar nawa za’a ciko ba dama dai don ya ji muryarta ne ya tabbatar itace ta turo.Daga nan aka fito da Musaddik da yaransa gaba daya. duk sun fita hayyacinsu, saboda duka da yunwa, sun yi bakinkirin kamar sun shekara a kulle. Bayan an fito da su, aka ba su kayan su da wayoyinsu, daga nan suka fito, anan ne Alhaji Hamza ya dubi musaddik yace "'Motata Musaddi& kawai za ta dauka, don ta yi maku kadan, ga wannan” .Ya dauko dubu biyar ya mika masu. "Duk da dare ya yi, sai ku san yadda za ku yi ku tafi gidajenku”. Suka karba suna