Page 155
godiya. Musaddik da Alhaji Hamza suka shiga mota, suka tafi,musaddik a jigace yake. Sun yi "'yar tafiya kadan, sannan Musaddik yadan dubi Alhaji Hamza Yace “Ashe ku na da alkawari, ai na dauka kuma duk kanwar ja ce?" Alhaji Hamza ya girgiza kai ya ce "*Hajiya Hudah ta shiga matukar damuwa a game da-halin da ka shiga, yau kwana biyu kenan muna billayin neman inda ka ke, sai Yanzu cikin daren nan, aka san inda ku ke. Ta kasa sukuni kwata-kwata. Naira dubu dari shida ta biya kudin belinku,” ya fadi kudin ne saboda yana son ya ci wani abu a ciki dubu dari biyu yasa ran zai ci.
Musaddik ya yi dan murmushi ya ce “Ta burgeni, don ina son mutum me cika alkawari, darajarta da kimarta' sun karu matuka a idona, ya labarin zabe?" Alhaji Hamza ya yi dariya ya ce “Komai ya yi dai-dai, domin Hajiya Hudah ta kara komawa kujerarta ta lashe zabenta a karo na biyu”. Ya yi murmushi cikin jindadi da farinciki ya ce. "To Alhamdulillahi." Alhaji Hamza ya dube shi ya ce. “Mu wuce can gidan Hajiyar ne, tunda dare ya yi, gobe ka karasa gida ko kuwa me ka gani?" Musaddik Ya dube shi ya ce “karfe nawa ne yanzu?”. Alh Hamza ya duba agogonsa yace “ karfe uku saura minti biyu “ ya gyada kai yace “Mu wuce gidan Hajiyar, duk da ba yau na saba yin dare na koma gida ba, kawai dai bana son na shigar ma matata gida a wannan lokacin da nasan tana cikin damuwa gara na shiga gida da safe ido na ganin ido” . Kafin Alhaji Hamza ya yi magana Haj Hudah ta kira wayarsa, da sauri ya dauka, tace “Kun taho ne?" Ya amsa "Eh, muna hanya
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM