Page 156
bamu dade da fitowa ba” ta dan yi murmushin farinciki tace “Ka gaya masa, idan babu damuwa ka wuto da shi gidana ya kwana, tunda dare ya yi, idan yaso gobe sai ya karasa gidansa”.Alh Hamza ya yi dan murmushi Yace “Na san za ki fi bukatar hakan, don haka na yi masa maganar hakan, ya kuma amince, zai taho yanzu haka muna kan hanyar gidan ki” ta kara murmusawa tace “Allah ya kawoku lafiya". Daga nan ta aje wayar. Har suka isa katon get din gidan Hajiya Hudah. Alhaji Hamza mamakin lamarin Hajiya Hudah yake yi. Wane irin gamon jini ne ya shiga tsakaninta da Musaddik. Me ya sa ta damu da lamarinsa? Suna isa. Mai-gadi ya bude masu get. A zahiri gidan Hajiya Hudah ya ba Musaddik mamaki, saboda kyansa, bama zaka fara hada shi da gidan ganawa da bakinta da musaddik ya taba zuwa ba, wannan gidan shine karshen zance. A gaskiya Hajiya Hudah ta aje. kudi. A hankali ya dubi Alhaji Hamza, bayan sun zauna a katon falon ta na kasa . "Yanzu wannan ma gidan Hajiya Hudah ne?” Ya gyada kai ya ce "Eh, wannan gidanta ne da take kwana a ciki, wancan da ka hadu da ita a ciki,ai kasan gidan ganawa da bakinta ne”. Musaddik ya jinjina kai yana kara kallon falon yace “Amma matar nan ta tara kudi ba kadan ba, siyasa ta karbeta, ta shekara hudu kan kujerar ta, ga shi ta kara komawa”. Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce. "'Hmmm! Ai Hajiya Hudah ba ta dogara kadai da