Page 157
siyasa ba, domin tun kafin ta shiga siyasa tana da matukar kudi……..? Bai karasa maganarsa ba, sallamar daya daga cikin masu yin hidimar gidan ta katse shi. Ta shigo cikin falon tana kallonsa.Tace "Sannunku da isowa, dama ku na ke jiran isowarku, domin na nuna maku inda za ku kwanta, ita Haj ta ce na gaya maku ta kwanta, sai gobe zaku hadu” Musaddik ya dubi Alhaji Hamza. A yayin da lokaci daya suka mike, sannan a hankali suka bi hadimar a baya. Har zuwa wani katon falo mai dauke da dakuna uku a ciki, kowannensu ta bude masa dakin da zai kwanta tare da ba su tabbacin za su sami duk abinda suke bukata a cikin dakin. Sai da suka shiga dakunan nasu sannan ta tafi. Shigar Musaddik dakin ya dade, yana kallon kayatuwar dakin, komai nq dakin na alfarma ne. Sai daya dumama cikinsa da ruwan Tea hade da wani daddadan Cake. Sannan ya shiga bandaki, wanka ya yi sosai, saboda tsananin tsamin da jikinsa ya yi, ga wari da yake yi Saboda datti jikinsa, har wani danko- danko yake yi, ba karamin dadi ya ji a jikinsa ba. Ya yi mamakin ganin riga da wando Kananan Kaya masu matukar tsada a jiye a cikin dakin, amma daya tuna abinda hadimar da ta kawo su dakin ta fada