Page 158
Sai ya daina mamaki, tunda ta ce duk abinda za su bukata, yana cikin dakin. Don haka ya aje nasa Kayan da suke surma uban wari, ya sanya wadanda ya gani a dakin ba tare da tunanin komai ba Sai Karfe hudu saura ya samu ya Kwanta .Asubar fari Musaddik, ya tashi ya yi alwala ya yi sallah, wanda rabonsa da yin hakan har ya manta.yana idarwa bai jira komai ba, ya fice zuwa falon Kasa a kofar farko, nan ya hadu da hadimar gidan, ta Yi masa kallon mamakin irin samamakon tashin da ya yi tace "Har ka fito haka da wuri?" Ya dubeta Ya gyada kai ya ce. "Eh, zan tafi ne, taimaka ki bude min kofa*. Ta wuce zuwa wajen kofar tana fadin "Me zance wa ranki ya dade, idan ta tashi? Ta bukaci zata ganku bayan ta tashi” ya yi mata kallon tsaf,yace "Ki gaya mata na tafi gida wajen iyalina domin suna bukatar sanin halin da nake ciki suma”, Ta jinjina kanta, lokaci daya ta bude masa kofar ba tare da tace uffan ba, yana rike da kayan da ya cire jiya a hannunsa. ya fice da gaggawa, duk da ba shi da ko Kwandala a aljihunsa. Haka ya. yi ta tafiyar sa a kasa tamkar wanda baya cikin hayyacinsa.