Musabbabi Book 1

Page 159

by @yargidanimam

Sai da gari ya gama wayewa tangaran! sannan MusaddiK ya isa gida, a zahiri Baba Mai-gadi ya yi matukar murnar dawowarsa. Afrah na zaune akan kujera Kuka take sosai, tun idar da sallar asubah dinta tana zaune kan sallayarta tana rokon Allah ya tsare musaddik a duk in da yake ,lokaci daya kuma takan dakata tayi kuka saboda fitar hawayen shine kesa ta ji abinda ya tokare kahon zuciyarta ya sauka.turo kofar da aka yi, ya sa ta yi saurin kallon kofar dakin. Musaddik ne ya shigo cikin sallama, ganinsa kamar daga sama ya sa Afrah ta mike zumbur ta na kallonsa daga sama har kasa,tana kallon yanayinsa na natsuwa babu alamar ya sha wani abu ga kayan da ke jikinsa, babu alamar musaddik ya na cikin wata masifa, a sanyaye ta kira sunansa “yaya musaddik”,ya amsa yana kokarin zaunawa akan kujera, zuciyarsa ta cika da tausayinta,domin kallo daya ya yi mata ya hango tsananin tashin hankali da damuwar da take ciki,wanda yasan shi ne sila. Sannan yana jin bazai iya jure irin kallon da take yi masa ba me cike da jin zafi da tuhuma. Ya mika hannunsa ya janyo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi yana cugaba da zuba mata tsararrun idanunsa masu kama da mayen karfe domin ji take yi a duk lokacin da ya tsareta da idanun tamkar ana fisgo kaunarsa ana sanyawa a cikin zuciyarta.bata raba daya biyu da gaske ne zuciyarta ta afka soyayyar musaddik soyayya kuma me karfi yadda yanzu take jin damuwarsa fiye da da. Itace ta fara kauda idanunta a cikin nasa gami da yin kasa da kanta,tace a sanyaye,cikin wata fuska me kunshe da damuwa tace “yaya Musaddik ina ka shiga, in dai lafiya kalau kaje ka yi zamanka ba tare da ka dawo gida ba, to ka dauki alhakkina idan har kasan lafiyarka kalau, don me ba za ka fahimtar da ni hakan ba, sai ka bar ni, ina wahala a kanka. Alhalin ka na cikin koshin lafiya. Na rantse da Allah ba ka kyauta min ba, ba ka kyauta ba...?” Ta barke da kuka, cikin damuwa da tashin hankali ya sanya hannu ya janyota zuwa kirjinsa ya rungumeta yana bubbuga bayanta da daya hannunsa alamar lallashi, ya dora bakinsa a kunnanta yana rada mata “kiyi hakuri bata miki rai shine abin da na fi tsana akan komai a rayuwata, kiyi hakuri “ kalamansa da irin rungumar da ya yi mata ya haddasama jikinta mutuwa, ji tayi tana bukatar kirjin da zata yi kuka don haka ta kara lafewa a jikinsa hawaye na cigaba da fita mata.