Page 160
Ya kara rungumeta shi ma yana jin irin abinda Afrah ke ji a ranta. Lokaci daya kuma ya na yi mata bayanin dalilin rashin dawowarsa gida, ya kara da cewa “Abinda ki ke zato ba haka bane, na san na kan kwana ba na gida wani lokacin amma ai muna magana ta waya, muna sanin halin da junan mu ke ciki, amma wannan karon tunda ki ka ji irin wannan shirun, ba ni ba waya, tabbas kin san ba lafiya ba, tunda ko ina nake ki yarda da ni Afrah ki na cikin raina da tunani na” Ta dago da jajayen idanunta tana kallonsa ta ce. tana kara kallon , amma sai yasa hannu ya kara kwantar da kanta akan faffadan kirjinsa, ta aje numfashi tace “Ba lafiya, ba amma jikin ka ai bai nuna haka ba, ga ka nan fes! Da sababbin kaya a jikinka” Ahankali ya cire hannunsa a bayanta, ya dagota sannan ya mike tsaye ya cire rigar jikinsa, ya juyo mata bayansa yace “Ki kalli bayana,ki gani” Afrah ta dago ta dora idanunta akan, bayansa ,duk a farfashe, wani wurin ma ya kumbura, ta mike a gaggauce tana fadin “Subahanallahi! Waye ya yi maka wannan aikin, wane mara imanin ne?"tana magana tana dora hannunta akan ciwon tana ji tamkar ta cire ta dawo da shi cikin jikinta. Ya juyo yana kallonta ya rike hannayenta ya maidota jikinsa ya kara rungumeta duka kan kujerar suka kara zaunawa yana rungumeta da ita cikin sanyin murya ya gama sanar da ita komai.
Ya dubi kayan jikinsa yace “'Hatta wannan kayan a gidanta na samu nasa Ita ce ta taimakeni ta fitar da ni daga wannan Kangin, ba don haka ba, yau din nan za"a kai mu Abuja, Idan ko aka kai mu wannan garin , sai yadda hali ya yi, domin ko miliyoyi ba zasu iya fitar da mu ba, kuma duk sai sun illata rayuwata kafin na fito , don haka Allah zamu yi ma godiya, sannan mu yi ma Haj Huda godiya ,domin ta bambanta da sauran yan siyasar da na sani da alama ita zata yi tausayi da amana.
Yar gidan Imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM