Page 161
Cikin hawaye Afrah ta sauke numfashi tace “Allah ya saka mata da alheri. ta taimake mu sosai” ta kara lafewa sosai a jikinsa, tana jin abubuwan da bata saba ji ba suna yawo a cikin jikinta,zuciyarta ta kara cika da kaunarsa,domin bata kara tabbatar ma da kanta ta fara son Musaddik ba so kuma na hakika sai da baya gidan. Ta yunkura tana son tashi,amma sai ya kara sa hannu ya janyota, yana tsareta da ido yace “ina zaki,bayan kinsan babu abinda na fi bukata sama da jin dumin jikin ki”, ta dago da idanunta ta dora a cikin nasa idanun, tana kokarin son gane ko shi ma ya fada irin tarkon da ta fada ne na soyayya, zuciyarta ta cika da fatan Allah yasa shi ma ya fara sonta ne. Ta dan dauke idonta a kansa tace “Ina son na je na samo maka ruwan zafi ne domin ka gasa jikinka,sannan kuma na samar maka abinda zaka ci”.
Ya matseta sosai yace “zan fi bukatar samun kulawarki ta musamman fiye da duk wannan abinda ki ka lissafa, sosai nake sha’awar ki Afrah”.ta ji kunya sosai ta sadda kanta kasa. Ya yi murmushi gami da mikewa tsaye ya tada ita tsaye, da kansa ya rufe kofar dakin sannan ya ja ta zuwa cikin uwardaki, bata yi musu ba, domin itama tana son abinda yake son yi din, musamman idan ta tuna rabon da ya kusanceta cikin kyakkyawan yanayi irin wannan harta manta.
Sai da suka kammala komai, hakanan Afrah ta rushe da kuka sosai, nan da nan musaddik ya gigice ya birkitota yana kallon yadda hawaye ke fita mata yace “me nayi miki?me yasa ki ke kuka kuma”. Ta lumshe idanunta ta bude tace “Nayi sha’awar ace kullum haka ka ke zuwa min cikin nutsuwa, tunda mu kayi aure ban taba jindadin kusantarka irin yau ba, baka cikin maye baka wari, yau cikin nagartarka ka fito min, na yarda kai jarumi ne yaya Musaddik don Allah ka taimake ni ka dawo cikin nutsuwarka”, shuru ya yi ko wace kalma da ta fito daga bakin Afrah tana gasa zuciyarsa, ya kasa cewa komai hakan yasa Afrah ta cigaba da magana cikin muryar tausayi. “Me ye amfanin wanna rayuwar, don Allah Yaya, don darajar Annabin rahama ka natsu, kai fa ba karamin yaro bane, ka dubi irin shekarun da ka ke da su, ka sani da kyar ne idan za ka Kara shekarun da ka yi a baya, ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da, rayuwa me dadi da tsafta irin wacce ka yi a baya Ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da,Ka yi yaki da shaidan. Ka rabu da abokanka na banza, ka koma ma abokanka na da, na-gari, ka yi tsaftatacciyar rayuwa, Ko ka dawo da kima da darajarka da ka rasa,wannan ba irin rayuwarka bace, ba ta kuma dace da kai ba ko kadan. Shin ya za ka yi da Yayanka idan ka fara haihuwa?" Ta kara nisawa tace “ina son yin rayuwa da kai har abada, a kalla ni ma yakamata na samu farinciki a gareka ko yaya ne, yanzu da kayi kwanaki a kulle ba ka sha komai ba ka mutu ne, me ka ragu da shi”. Kamar daga sama kawai ta ji Musaddik ya saki ajiyar zuciya yace “Na sha, ko da nake kulle Afrah na sha domin ba zaki gane halin da nake ciki ba ko nace bazan sha ba ji nake kamar za’a cire raina idan ban sha ba”. Jikin Afrah ya yi sanyi kalau, ta dago ta na kallonsa sosai tace “kana rufe ta yaya ka samu kayan maye ka sha?”. Ya runtse idonsa da karfi ya bude yace “A cikin ma’aikatan yansandan muke samun me sayo mana duk dare, mu kan sha kuma lafiya lau ba tare da wata matsala ba, domin ko da safe ba’a ganewa saboda muna kiyayewa”. Tirkashi lalle al’amarin kasata ya kazanta abinda Afrah ke fada a ranta kenan wajen hora masu laifi anan ake ba mutum kayan lefi ya yi amfani da shi, to ta ina za’a iya samun gyara. Musaddik ya tashi ya nufi bandaki yana cewa “Addu’a kawai nake bukata Afrah domin duk duniya babu wanda ya kaini son shiryuwa, ki kara hakuri mu jira lokaci kawai, domin na fiki kosawa na sami shiriya”. Ya tsaya a bakin bandakin ya na juye da bayansa ya cigaba da cewa