Musabbabi Book 1

Page 162

by @yargidanimam

"Ko Ki na tunanin wannan abin baya damuna ne? To duk duniya na rantse miki banda wata damuwa sama da wannan, ina cikin matsananciyar damuwa, domin tun bayan aurena da ke Burina bai wuce na kintsu ba, saboda na san abinda ki ka yi min na aurena a l Lokacin da babu wata mace me hankali irinki da za ta iya aurena.a salima ban taba jin zan iya yin komai domin na shiryu ba sai bayan da na aure ki Amma abin mamaki na kasa barin koda abu daya, wannan lamari yana matukar damuna gami da daure min kai”. Ya karasa magana cike da damuwa sannan ya dan waiwayo ya dubeta yace “ki yi hakuri ki yi min afuwa”. Afrah ta ce ta na me cike da jin tausayin sa, “Tunda har kana son ka daina, to ina son ka sa ma ranka zaka iya bari, ka yaki shaudan sannan kuma ka jajirce, ka sani duk abinda ka ga mutum bai daina ba to baisa kansa ba ne, zaka iya yaya musaddik,kuma Allah zai taimake ka, a kullum ka tuna kai maraya ne a yanzu iyayenka na bukatar addu’ar ka amma nasan ko lokacin addu’ar ma ba ka da shi, yakamata ka taimaki kanka Ka dawo cikin tunaninka Dukiyar da mahaifinka ya bar maka, ba ka kirkinta ba, rashin natsuwarka ya sa an rabaka da komai, saboda an san babu abinda za ka iya yi, don ba ka amfani kanka ba ma, balle ka amfani dukiyarka wannan babu inda zai kai ka. Shekara da shekaru ka na cikin wannan mugun hali, ba ka ko tunanin gaba” Maganganunta sun yi tasiri a zuciyarsa, ya ji yana neman ya tsani kansa ya numfasa ya sa hannu ya bude kofar bandakin har zai shiga sai ya kara tsayawa, sai kuma ya juyo ya dawo gefen gadon ya zauna. “Duk maganganunki hakane, kuma ke ma ba zaki gane halinda nake ciki ba