Musabbabi Book 1

Page 163

by @yargidanimam

Shi ya sa ban so a kashe rayuwarki ta hanyar aurena ba, na san ba ki dace da ni ba, ba ni ya kamata ki zauna ki yima biyayya gami da bauta ba a matsayin mijinki, ban so ace nine me cutar da ke ba, ki na da wani matsayi a guna na musamman da duk bata miki da nake yi nakan ji abin har cikin jinina na kan ji damuwar da tafi taki, bansan dalili ba, amma dai nasan ke ta musamman ce, kin yi hakuri Domin na san a iya tsawon lokacin da ki ka dauka tare da ni. Ba ki taba samun wani farin-ciki daga gareni ba, ban taba faranta miki ba, don haka bai kamata na ci-gaba da tauye r rayuwarki ba, Hakan ya sa zan kawo wata shawara tsakanin mu."

Afrah ta kara goge hawayen da ya fara fita mata, saboda tausayin musaddik, ta tattaro ta tashi ta zauna sosai tana kallon yadda babu wasa a fuskar Musaddik alamar maganar da yake son su yi babbace, kila kuma mai muhimmanci ce, a hankali ta ce "Wace irin shawara ce?”

Ya dan gyara zamamsa gami da hadiye wani zazzafan yawu, alamar shi kansa abinda yake son ya furtan, ba me dadi bane a gare shi, kuma da alama ba don kansa zai kawo maganar ba, kila don sadaukarwa irin ta yadda ya fassara yadda Afrah take a gare shi. ya dade yana kure mata da ido sannan tamkar yana jin shakkar furta abinda yake son furtawa, sannan yace "Ba wata shawara bace Afrah face Shawarar rabuwa da junan mu”,

Gaban Afrah ya yi mummunan faduwa domin jin maganar da bata taba zaton jinta daga bakinsa ba, Ta yi gaggawar kallonsa gami da bude baki, tana maimaita kalmar rabuwa. Ya gyada kai yace “Eh saboda bai kamata ki lalata rayuwarki don ki gyara rayuwata ba, kamar yadda ki ke son ki ganni cikin farinciki na rantse miki haka nake so na ganki cikin farinciki, yadda ki ke son rayuwata ta yi kyau haka nake son taki rayuwar ta yi kyau, duk yadda ki ke jin kin damu da ni haka ni ma nake jin na damu da ke “. Ya kara kallonta damuwa da tashin hankalin da ya gani shimfide kan fuskarta yasa ya ji zuciyarsa ta yi duhu sai dai duk da haka bai fasa cigaba da jaddada maganarsa ba “amma zan ba ki kwana biyu, ki yi tunani Domin babu abinda zan iya zartarwa sai da amincewarki amma ina son idan za ki yi tunanin, ki cire tausayina ki aje shi a gefe, domin na san shi kadai ne a ranki, ba so na ba Ki sa a ranki hukuncin da za ki yanke me kyau, shine zai ba ki damar auran wanda ki ke so, kuma yà dace da rayuwarki, ki haifi 'ya'ya daga