Musabbabi Book 1

Page 164

by @yargidanimam

tsatson uba na-gari. Don Allah kada ki yi tunanin tausayina da taimako na a cikin tunanninki, ni kuma duk abinda ki ka yanke, da shi zan yi amfani." Ya kara kallonta, ya ci-gaba da cewa “Haka zalika kada ki damu da maganar kawu,ni zan fahimtar da shi komai, ba kuma zai taba ganin laifinki ba, a cikin wannan tunanin da nake son ki yi Tunanin makomar rayuwarki kawai za ki yi." Bai damu da kallon kaduwa da mamakin da take yi masa ba, ya tashi kai tsaye ya shige bandaki domin ya yi wanka. Ta dawo da kallonta ga cikin dakin da ta ga gaba daya ya na juya mata.ya aje wayarsa. Idanunta suka kara cika da hawaye. Ta yaya za'ayi Musaddik ya fara tunanin rabuwa da ita, har wane tunanin za ta yi wanda ba ta yi shi ba kafin auransu? Tabbas a da tausayinsa ne kawai a cikin zuciyarta, amma yanzu sonsa ya riga ya cika dukkan zuciyarta, ba ta jin akwai wani abu da zaisa ta rabu da shi, idan tunaninsa tausayinsa ne kawai a ranta to ya yi kuskure, domin duk da bakin halinsa shi zuciyarta ke so yanzu matukar so.