Musabbabi Book 1

Page 165

by @yargidanimam

Ita ko Hajiya Hudah bayan tashinta, babu wanda ta tadda cikin musaddik da Alh Hamza, domin shi ma Alh Hamzan bayan tashinsa da ya fahimci Musaddik din ya tafi , shi ma sai ya tattara ya nufi gidansa, sosai ran Haj Hudah ya baci, domin ita kanta ba ta san dalilin daya sa take kwadayin Kara son ganin Musaddik ba a rayuwarta. Ta kira wayarsa, ya fi a kirga, amma wayarsa tana kashe. Daga bisani dai da hakurinta ya gaza dole ta kira Alhaji Hamza sosai ta nuna masa bacin ranta na rashin jiranta, da su kayi ta fito.sannan ta umarce shi daya gayyato Musaddik Party din da za su gudanar a gobe, tunda dama dawowar Musaddik din kadai take jira su yi party domin nuna murnarsu na cin zabensu. Alh Hamza Ya ba ta hakuri tare da yi mata alkawarin gayyato Musaddik kamar yadda ta bukata.wanda zuwa wannan lokacin Alh Hamza ya daina mamakin irin damuwar da Haj Hudah ke yi da musaddik ya sama ransa Allah ne dai ya dora Musaddik din a kanta kawai.

Malam Mahmud kuwa tun da sassafe ya fita ya je (Police Station) da yawa, amma bai dace da samun Musaddik ba ga shi ya kwana wayarsa babu caji hakan yasa duk irin kiran da Afrah ta yi masa domin ta sanar da shi dawowar Musaddik bata yi nasarar samunsa ba.sai azahar ya yanke shawarar dawowa gida, domin ya ci abinci ya kuma dan huta sannan ya kara fita. Zuwa lokacin kuwa Inna Halima itama tana can cikin muguwar damuwa domin tun safen kafin ya wuce sai da ya shiga gidanta ya sanar da ita abinda ke faruwa, itama kuma duk motsi saita kira wayarsa domin ta ji halinda ake ciki amma wayarsa na kashe. Yayi sa’a ya tadda akwai wuta hakan yasa yana shigowa gidan ya sanya caji. Mama Hauwa kuwa sai kaiwa take tana komowa cikin rashin nuna danuwarta akan duk abinda yake faruwa, domin har cikin ranta tana ganin mallam Mahmud ya so ba kanshi wahala ne kawai don babu wani amfanin fita neman musaddik mutumin da ya saba yawon tambadarsa. Sai dai bata furta komai ba domin yadda ta ga fuskar mijin nata idan ta sake tayi masa maganar da bata gamsar da shi ba zai iya ci mata mutunci.

Mallam Mahmud ya na idar da sallar azahar ya kunna wayarsa, kamar ana jira ya kunna ,Kiran Afrah ya shigo cikin Wayar, da sauri ya dauka, bayan sun gaisa ne, cikin natsuwa ta gaya masa tana ta neman wayarsa ta sanar da shi dawowar Musaddik da kuma abinda ya faru, amma wayar tana kashe Malam Mahmud ya numfasa cikin yi ma Allah godiya.

Yar gidan Imam MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM