Musabbabi Book 1

Page 166

by @yargidanimam

Mallam Mahmud ya gyara zamansa, ya tsinci damuwa a cikin muryarta sosai, don haka yace, “ki yi hakuri Afrah ko wane bawa akwai irin kalar tasa kaddarar, don haka ina son ki sa a ranki wannan itace irin taki kaddarar,kuma kada ki yanke tsammanin samun shiriyar musaddik ki sa a ranki shi komai lokaci ne. Don haka idan Allah ya kawo iyakar lamarin,Shi kenan, sai ki ga kamar ma ba'a taba yi ba. shiriya da batarwa duk suna hannun Allah, kuma duk wanda Allah ya batar. Idan duk duniya za ta taru ba su isa su shiryar da shi ba, wanda kuma ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi, komai yana hannun Allah Shi ya sa ya ce mu yi imani da kaddara me kyau ko mara kyau. Saboda haka ki sa Musaddik da lamarinsa a matsayin kaddarar rayuwarki, ki yi hakuri, ki yi komai domin Allah, sai ki ga Allah ya taimakeki. Ki ci-gaba da yi masa nasiha gami da addu'a tare da biyayya a matsayinsa na mijinki, Wanda duk lalacewarsa Aljarnarki tana Karkashin kafarsa ne”. Cikin hawaye gami da sanyin jiki Afrah ta ce. "Na ji, nagode Baba kuma za ka sameni me biyayya tare da tsare dokokin aurena". 'A hankali yace “Allah ya yi miki albarka, ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira”, cikin jindadin addu’ar tace “Amin Baba”.sannan suka aje wayar lokaci daya. Mama Hauwa da take tsaye tun bayan daya fara wayar, ta yamutsa fuska ta wuce dakinta ba tare da tace uffan ba.