Musabbabi Book 1

Page 167

by @yargidanimam

Domin tun daga ranar da Malam Mahmud ya yi mata takarar kada ta Kara shiga harkar Afrah da auranta, ta daukar ma kanta alkawarin ba za ta kara sa bakinta , a komai ba.Ko da ko me zai faru,. Hakan ya sa duk da ta san meke faruwa, ba ta yi magana ba, domin tasan ko da tayi maganar ma duk fushinsa a kanta zai juye.shi yasa ko jajantawa ba ta yi ba.Babu abinda ya dameta.

Afrah kuwa tun bayan wayar da tayi da mahaifinta sai ta ji ta kara samun kwarin guiwa akan aurenta da Musaddik, damuwar da take ciki na maganar rabuwa da Musaddik ya yi sai ta ji ta ragu a zuciyarta, domin bata jin a yanzu akwai wani dalilin da zaisa ta iya rabuwa da Musaddik domin da zata iya rabuwa da shi da tun farko ma bata aure shi ba.

Haka zalika ta yi mamakin yadda Musaddik ya ki fita ko'ina, tun bayan dawowarsa, bayan da ya yi wanka barci Kawai yake yi, ko wayarsa bai bude ba. Hakan ya sa bai san irin neman wayarsa da Alhaji Hamza yake yi ba, har sai wajen karfe goma na dare daya bude wayarsa, yana budewa, wayar Alhaji Hamza tana shigowa.Bayan ya dauka, tambaya Alhaji Hamza ya jefo masa,

“Meye dalilin kashe wayarka? bayan ka tafi ba tare da ka yi sallama da kowa ba?" Ya dan runtse idanunsa yace "Na gaji ne, barci na yi, shi ya sa ban bude wayar ba, ya aka yi ne Alhajin Allah?' Daga nan Alhaji Hamza ya gaya masa bukatar Haj Hudah na amsa gayyatar Party din murnar cin zabenta, da za’a gudanar a gobe,Musaddik ya jinjina kai Yace "Karfe nawa ne goben?”, Yace "Karfe bakwai na dare wannan gayyatar ta musamman ce, da fatan za ka amsa"Ya gyada kai ya ce. "Babu damuwa Allah ya kaimu goben”. Daga nan suka yi sallama. Hakika yana son mutum me cika alkawari, daga dukkan alamu kuma