Musabbabi Book 1

Page 168

by @yargidanimam

Hajiya Hudah mace ce me cika alkawari, da alamar wannan gwarnatin za ta amfane shi.

Washegari kuwa tun karfe bakwai da rabi, Musaddik ya isa tankasheshen (Hall) din da ake gabatar da liyafar, haka zalika duk da dimbin jama'ar da ke wajen, sai da Musaddik ya samu tarba ta musamman daga Hajiya Hudah. Wacce ta ci kwalliya da kaya masu matukar daukar hankali. Daga wuyanta zuwa kunnenta da yatsun hannayenta duk zinare ne, sai daukar ido suke, ta sha kyau har ta gaji. Cike da farin-ciki da annashuwa ta dubi mutumin da ke gefenta, wanda shi ma yake cikin shiga ta alfarma, ya tsare gida, ta nuna Musaddik ta ce, cikin murmushi "Yallabai ga mutumin da na ke ba ka labarinsa da irin taimakon da ya yi min tun a waya Musaddik”. Mutumin ya dubi Musaddik ya yi masa kallo daga sama har Kasa,fuskarsa ta canja wani yanayi irin yanayi me wuyar fassara, sannan ya ce "Sannu Musaddik mun gode da kokarinka, duk da komai an yi shi ba na nan, to na sami labarin duk kokarin da ka yi da kuma hatsarin da ka tsallake, sannu da kokari", ya karasa magana yana kara Kafe idanunsa akan kyakkyawar fuskar Musaddik, wanda ya yi dan murmushi, domin ya jidadin yadda a yau aka maida shi mutum mai daraja, wanda rabonsa da ganin hakan har ya manta, ya dubi mutumin ya ce "'Haba ai babu komai, ni ma nagode, da irin taimakon da Haj tayi min”.

Hajiya Hudah ta dubi Musaddik, tana kokarin gyara zamanta ta ce “Musaddik wannan shine mijina Alhaji Yusuf sanda”