Musabbabi Book 1

Page 169

by @yargidanimam

Musaddik ya yi gaggawar Kara bude idanunsa sosai cike da matsanancin mamaki, ya Kara duban Alhaji yusuf sanda yace “Mijinki?" Ta amsa masa da "Eh, shine mijina”, ya kara kallonsa yace "Sannu Mai-gida, da fatan kana lafiya? “, Alhaji Yusuf Sanda ya kara kura masa ido tamkar yana wani tunani, sannan ya ce "Lafiya kalau Musaddik." Daga nan musaddik ya wuce a hankali zuwa kujerar da zai zauna, a yayin da Alhaji Yusuf Sanda ya bi shi da wani irin kallo da shi kadai yasan dalilin yi masa irin kallon. Har aka yi liyafar nan aka tashi Musaddik yana cikin matukar mamakin Kasancewar Haj Hudah matar aure, domin koda wasa bai taba kawowa a ransa cewa Hajiya Hudah Matar aure bace, domin babu alamar hakan. Kwarai musaddik ya so kebewa da Alhaji Hamza, don kuwa haka nan ya ji har cikin ransa yana son sanin wasu abubuwa game da Haj Hudah Amma hakan bai samu ba har sai da ya yi sallama da Hajiya Hudah, da nufin tafiya gida ta kuma gaya masa ta na son ganinsa gobe karfe sha biyu na rana, kafin ta wuce zuwa Abuja. Musaddik Ya kan rasa irin kallon da Alhaji Yusuf Sanda yake tsare shi da shi, da ya rasa dalili, domin ko ya ya ya juyo idon sa kawai ya ke gani a kansa.Sai da zai tafi ne, sannan Àlhaji Hamza ya dauke shi domin ya kai shi gida kamar yadda Haj Hudah ta bashi umarni.