Page 170
A lokacin kuwa karfe biyu saura kwata ne na dare, sun dan yi nisa da fara tafiya, sannan hakurin Musaddik ya gaza, inda ya dubi Alh Hamza yace "Alhajin Allah, dama Hajiya Hudah matar aure ce?”. Alhaji Hamza ya dan saki numfashi, gami da ƙara riƙe sitiyarin motar sosai sannan yace "Matar aure ce mana, kai ba ka san hakan ba ne sai yau” Musaddik Ya girgiza kai ya ce. "Ban san hakan ba, ban kuma taba tsammanin hakan ba, domin kai kasan ban dade da fara yin hulda da ita ba, kuma kai na sani akan harkokinta Tunda kai ne ka nemeni akan aikin nata, Sannan kuma yanayinta da yadda take gawurtacciyar yar siyasa da yadda take gogaggiyar mace, gaskiya ban taba tsammanin mace irinta za ta iya zaman aure a karkashin wani ba, musamman ma yadda take da masu gidan rana a hannunta." Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce "'Haka ne maganganunka, amma lalle ka na bukatar ka san wace ce Hajiya Hudah, domin ka kore ma kanka shakka akan rayuwarta, amma dare ba zai ba mu damar na tsaya na gaya maka wacece ita ba.Sai dai abu daya zan gaya maka, tabbas duk da dukiyar da Allah ya ba ta, to fa Allah ya jarabceta da son yin aure, domin cikar kamalarta da take kokarin nunawa duniya ita me kirki ce, duk kuma da kasancewarta yar siyasa to tana son aure, kuma wannan siffa da ta fito da ita ta taimaka wajen kara mata yawan masoya a harkar siyasarta,kuma tabbas Alhaji Yusuf Sanda a yanzu shi ne mijinta”. Musaddik ya dubi Alh Hamza cike da gamsuwa akan maganar sa sannan yace “To amma a matsayinsa na mijinta, me ya sa ba'a san shi ba,
Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM