Musabbabi Book 1

Page 171

by @yargidanimam

musamman akan lamuranta na siyasa, me yasa kuma har muka sami damar kwana a cikin gidansa, ba tare da mun gan shi ba, sannan duk harkokin siyasarta, me ya sa babu shi a ciki?" Shi kansa musaddik baisan dalilin irin wannan tambayoyi ba da ya ke zubama Alh Hamza ba. Cikin rashin damuwa da tambayoyin na sa Alh Hamza ya amsa masa da cewa, “mun kwana a cikin gidansa ne, a dalilin a ranar baya ma kasar, yau din nan da rana ya sauka, yana Paris, duk wannan badakalar siyasar da ake yi bayanan, nasan kuma da yana nan da komai da shi za’a yi”.Musaddik ya dan dube shi yace “Me yake yi a Paris? Da ya fi masa muhimmanci fiye da shiga harkar matarsa, a lokacin da take da bukatarsa?" Zuwa lokacin Alh Hamza ya fara jin wani iri akan irin tambayoyin da Musaddik ke yi masa, a kan Haj Hudah, da mijinta. Duk da haka ya yi kokarin amsa masa yace “Saboda can din ma aikinta yake yi, domin kusan shi yake rike mata da kasuwancinta da take gudanarwa a kasashen waje, don haka bai cika zama ba a Najeriya, Kusan duk sabgoginsa ya fi yin su a kashashen waje”. Musaddik ya jinjina kai, ya yi shiru ne Kawai ba don wai tambayoyinsa sun kare a kan Hajiya Hudah ba, a'a sai don bai ga dalilin da zai zauna yana tambaya akan matar da baida wata dangantaka da ita ba, don haka ya ja bakinsa ya tsuke har suka kai Kofar gidansa Sannan ya sauke shi ya yi ma Alh Hamza godiya, gami da sallama sannan ya shiga buga get din, yana son a bude masa.Baba Mai-gadi ya taso da sauri domin sanin babu wanda zai buga gida a wannan lokacin sai musaddik, ya na bude masa kofar ya tsaya yana kallonsa,lokacin da yake shigowa abu daya ya yi ma Baba Mai-gadi dadi, shi kuma ya hana ya yi Masa fada kamar yadda ya saba kullum, wato ganinsa cikin hayyacinsa, babu alamar ya sha wani abu balle ya bugu, sai dai abinda bai sani ba ya sha abubuwansa sai dai ba da yawa ba, hakan yasa bai fita hayyacinsa ba.